Gwamnatin Tarayya ta kai ziyarar ta’aziyya Kano kan rasuwar Ɗantata

Spread the love

A ci gaba da nuna alhini kan rasuwar fitaccen ɗan kasuwa kuma jigo a Arewacin Najeriya, Marigayi Alhaji Aminu Dantata, wata tawagar gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ta kai ziyarar ta’aziyya zuwa jihar Kano domin halartar zaman makokin.

Tawagar ta haɗa da fitattun jami’an gwamnati irinsu mataimakin shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Sanata Ibrahim Hassan Hadejia; Mai ba shugaban kasa shawara kan ayyukan ƙasa, Dr. Aliyu Modibbo; da kuma tsohon ministan shari’a, Dr. Mohammed Bello Adoke. Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, tare da wasu daga cikin manyan jami’an gwamnati, sun tarbi tawagar inda suka ɗunguma zuwa gidan Marigayin domin nuna girmamawa.

A yayin ziyarar, mataimakin shugaban ƙasa ya gabatar da addu’o’in neman rahamar Allah ga Marigayin, tare da jajanta wa iyalansa da ‘yan uwa bisa wannan babban rashi. Ya kuma tabbatar musu da cewa gwamnatin Tinubu na tare da su a wannan lokaci mai cike da juyayi da alhini.

By ukarofi