Matan Ribas sun caccaki Wike bisa zargin matar Amaechi da hannu a badaƙala

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ƙungiyar Matan Ribas ta Ƙasa (RIVSWAN) ta yi alla-wadai da zargin cin mutunci da Ministan Abuja Nyesom Wike ya yi akan matar tsohon gwamnan jihar, Rotimi Amaechi, wato Dame Judith Amaechi.

Ƙungiyar ta hannun Shugabarta ta riƙo, Ichechi Welendu, ta yi martani ga kalaman ministan, waɗanda ya yi su a wata hira da gidan talabijin, inda ya yi zargin cewa Hukumar Kula da Yankin Neja-Delta (NDDC) tana biyan Dame Amaechi Naira biliyan 4 a kowane wata domin horar da matan yankin.

A sanarwar da ta fitar, ƙungiyar ta bayyana zargin ministan a matsayin abinda aka ƙirƙira da ba shi da asali ba tare da la’akari da haɗarinsa ba, tana mai kira ga al’umma da su ƙaurace musu.

Ta kuma ce, baki ɗaya zargin da ya yi akan matar tsohon gwamnan abin dariya ne kuma tozarci ne ga al’umma duba da cewa ba a gian su akan hujjoji ba.

Ƙungiyar ta yaba wa Dame Ameachi kan ayyukanta na alheri da suka haɗa da kyautata wa al’umma da ingata su ta shirin bada tallafin inganta al’umma na (ESI).

Har’ilayau, RIVSWAN ta bayyana cewa Dame mace ce da ta ƙarar da dukiyarta wajen inganta rayukan mata a Neja-Delta, don haka ba daidai ba ne al’umma ta ruɗu da zargi da aka yi akanta marasa tushe ko makama.

By Babaji