Tinubu ya aiki Shettima zuwa dubiyar Buhari a London

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yana karɓar magani a wani asibiti dake London a Ingila, kamar yadda rahotanni da dama suka bayyana.

Akan haka ne Shugaba Bola Tinubu ya umarci mataimakinsa, Kashim Shettima da ya je ya duba halin da tsohon shugaban ƙasar ya ke ciki.

Muryoyi sun shaida cewa, an shirya tafiyar Shettima zuwa duba Buhari mai shekaru 81 ne a ƙarƙashin umarnin Shugaba Tinubu.

Lamarin rashin lafiyar, wanda ba a bayyana asalin abinda ke damunsa ba, ya janyo hankulam al’ummar Nijeriya, lamari da ya sa ake cecekuce a kai.

Saidai, makusantanasa sun bayyana cewa yana halin farfaɗowa daga rashin lafiyar da ya ke fama da ita a yauin karɓar maganin .

Da fari, an shirya tafiyar Shettima zuwa Addis Ababa na ƙasar Habasha ne, wadda Framinista Abiy Ahmed ya gayyace shi zuwa taron buɗe shirin ingata muhalli na ‘Green Legacy Initiative’.

Amma, Kakakin Shettima, Stanley Nkwocha bai fitar da wani jawabi game da lamarin ba, zuwa lokacin kammala wannan rahoton.

Ana ganin raɗe-raɗin cewa jikin Buhari ya yi tsanani ya sa tsohon mataimakinsa kan harkokin yaɗa labarai ta kafafen zamani, Bashir Ahmad ya yi gamsassun bayanai akan halin mai gidan nasa ya ke ciki, a wani saƙo ta Facebook.

By Babaji