
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Yayin da Majalisar Dokoki ta matsa wa Babban Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL) game da lamarin wasu maƙudan kuɗaɗe, a ranar Alhamis ne Shugaban kamfanin, Bayo Ojulari ya sake gaza amsa gayyatar Kwamitin Asusun Ƙasa na Majalisar Dattawa.
Wannan shi ne karo na biyu da Ojulari ya ƙi zuwa zauren majalisar domin amsa tambayoyi akan Naira tiriliyan 200 da aka gaza bada gamsassun bayanai akansu acikin rahoton kuɗaɗe da kamfanin ya fitar.
A madadin zuwa da kansa, Ojulari ya naɗa wata tawaga domin ta wakilce shi, inda Majalisar Dattawan ta ƙi sauraron su tare da haƙiƙancewa sai shugaban ne da kansa za ta saurara akan batun.
Kwamitin, ƙarƙashin jagorancin Sanata Aliyu Wadada (Nasarawa ta Yamma) ya bayyana rashin ganin Ojulari a matsayin rashin girmama matsayin majalisa da kuma saɓa wa hukuncin dokar ƙasa.
Da ya ke jawabi, Wadada ya bayyana ce “Mu na magana ne akan N200trn, kuɗin da ya kai kusan ninki 10 na kasafin Nijeriya na 2024”, lamarin da ba abin da za a turo wakilci a kai ba ne.
A kwanakin baya ne majalisar ta bada wa’adin kwana 10 ga Ojulari da ya gurfana a gabanta don bada gamsassun bayanai akan yadda aka yi da kuɗaɗen, waɗanda ta shirya tambayoyi 11 akan su.
