Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Ma’aikatar lafiya ta tarayya da ta Jiha, tare da abokan hulɗar su, zasu ƙarfafa yaƙi da cutar zazzaɓin cizon sauro a jihar.
A wani babban mataki na ƙara ƙaimi a yaƙin kawar da cutar zazzaɓin cizon sauro a Katsina, gwamnatin kihar ta karɓi tarin kayayyakin rigakafin cutar, ciki har da gidan sauro sama da miliyan 4.5 da sauran kayayyakin magance cutar daga shirin nan na kawar da zazzaɓin cizon sauro na Ƙasa (NMEP) da haɗin gwiwar da Global Fund.
Kayayyakin sun haɗa da gidan sauro masu magani, kayan gwajin cutar da kuma magunguna, waɗanda aka samar ta hanyar tsarin saye na ƙasa tare da goyon bayan ƙungiyoyin Society for Family Health da Catholic Relief Services (CRS).
An gudanar da bikin miƙa kayayyakin a wani taro da ya samu halartar jami’an lafiya daga matakin jiha da wakilan hukumomin lafiya na ƙasa da ƙasa.
Ms. Ayodele Shakira, wakiliyar NMEP, wadda ta wakilci shugaban shirin na ƙasa, ta miƙa gaisuwa tare da yabawa goyon bayan da jihar Katsina ke bayarwa. “Muna farin cikin miƙa waɗannan kayayyakin kiwon lafiya da suka haɗa da gidan sauro masu magani domin tallafa wa yaƙin kawar da zazzaɓin cizon sauro a jihar.
Ta bayyana cewa an samar da su ne da kuɗaɗen Global Fund ta tsarin gwamnati,” in ji ta.
Da yake karɓar kayayyakin, kwamishinan lafiya na Jihar Katsina Hon Musa Adamu Funtua, ya nuna gamsuwa da matakan da aka ɗauka tare da tabbatar da amfani da kayayyakin yadda ya dace.
Ya bayyana cewa gwamnatin Katsina ta duƙufa wajen ganin an cimma burin wannan gangami. “Mun himmatu wajen ɗaukar nauyi da bada haɗin kai domin wannan aikin ya sami nasara wannan lokaci da ya dace,” in ji Funtua.
Shi kuwa ɓangaren, wakilin Catholic Relief Services (CRS), Mr. David Dedanila, ya ja hankalin al’umma da hukumomi da su tabbatar da cewa an yi amfani da kayan bisa tsari. “Duk da cewa an bayar da waɗannan kayayyakin kyauta ne, an sayo su ne da harajin jama’a daga sassa daban-daban na duniya,”kwamishinan ya ce.
Don haka yana da muhimmanci a cewar sa a tabbatar da an yi amfani da su yadda ya kamata domin yaƙar cutar.
Kayayyakin da aka karɓa sun hada da: gidan sauro guda 1,492,921 na ƙananan hukumomi 11 a yankin Katsina (Katsina zone) sai yankin Funtua guda 1,472,000 da yankin Daura gidan sauro (Mosquito nets guda 1,554,677
An adana su a manyan ɗakunan ajiya uku da ke Katsina, Funtua, da Daura, domin rabawa a cikin ƙananan hukumomi 34 da ke fadin jihar.
Ana sa ran fara rabon kayayyakin nan bada jimawa ba.
