Ambasada Yahaya Kwande ya karɓi sandar sarautar Long Kwo

Spread the love

Daga HABU ƊAN SARKI a Jos

Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang ya miƙa sandar sarautar Masarautar Kwo da ke Kwande a ƙaramar hukumar Qua’an-Pan ga Miskom Yahaya Kwande, a matsayin sabon Long Kwo na 28.

A wani gagarumin taro da aka yi a garin Kwande, wanda ya samu halartar manyan baƙi daga sassan ƙasar nan daban-daban, Gwamna Mutfwang wanda ya samu wakilcin kwamishinan kula da masarautun gargajiya da ƙananan hukumomi Ephraim Usman, ya bayyana cewa, wannan sarauta ta Long Kwo tana da matuƙar muhimmanci ga tarihin masarautun gargajiya a Jihar Filato.

Ya ce, sarakunan gargajiya na da matuƙar muhimmanci ga cigaban zaman lafiya da haɗin kan al’ummar jihar nan, a yayin da gwamnatin sa ke ƙoƙarin ganin dukkan masarautun da aka jima ba a cike gurbi su ba a faɗin jihar nan, an samar da waɗanda suka cancanta su riƙe su.

Gwamnan ya kuma jaddada cewa, miƙa sandar sarautar da aka yi wa Alhaji Yahaya Kwande, musulmi na farko a wannan masarauta, bayan tsawon lokacin da aka yi ana taƙaddama akan kujerar sarautar, shaida ce da ke ƙara nuna aniyar gwamnati samar da ingantaccen zaman lafiya, da kimar saurautun gargajiya a jihar.

Shugaban ƙaramar hukumar Qua’an-Pan, Christopher Manship ya yabawa Gwamnan Jihar Filato bisa jajircewarsa wajen ganin an cike gurbin da aka daɗe ana jiran wanda zai maye shi, a masarautar Kwo.

Sabon basaraken, Miskom Yahaya Kwande ya yi wa Gwamna Caleb Mutfwang bisa damar da ya bashi na cimma burin da ya daɗe da shi a rayuwarsa, don ganin ya gaji sarautar gidansu.

A ranar 11 ga watan Maris na wannan shekara ne Gwamnan Jihar Filato ya ayyana Alhaji Yahaya Kwande a matsayin sabon basaraken Masarautar Kwo.

By ukarofi