Ambaliya: Ku koma yankuna masu tudu – Gwamnan Neja ga al’ummar ƙauyuka 2,000

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamna Mohammed Umaru Bago na Jihar Neja ya kirayi al’ummar ƙauyuka sama da guda 2,000 dake kusa da rafuka da wuraren da ke da barazanar ambaliya da su ƙaura zuwa yankuna masu tudu.

Bago ya yi wannan kira ne a wata takarda ta hannun ofishin mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Jonathan Vatsa, ranar Juma’a.

Ya ce, akwai buƙatar al’ummar da ke ire-iren yankunan ylsu kiyaye gargaɗin Hukumar kula da Yanayi ta Ƙasa game da yiwuwar aukuwar ambaliyar ruwan sama a wasu yankunan faɗin Nijeriya.

A kwanakin baya ne hukumar ta yi hasashen samun ambaliya a wannan watan a sassan wasu jihohi guda 15 ciki har da Neja, don haka aka buƙaci al’umma su ɗauki matakan kauce wa iftila’in.

Gwamnan ya kuma ce, Ma’aikatar Kula da Muhalli ta Ƙasa ta cibiyar gargaɗi ambaliya a rashen kula da yankunan ruwa, ta yi gargaɗin samun ambaliya a wasu sassan jihar, yana mai cewa lallai sai jama’ar da hakan ya shafa sun kiyaye.

Ya ƙara da cewa, Gwamnati ba ta fatan sake samun irin ambaliyar da ta auku a Ƙaramar Hukumar Mokwa a watanni kaɗan da suak gabata, lamarin da yayi sanadin rasa rayuka da dama, ɗaiɗaita al’umma da lalata dubunnan gidaje.

By Babaji