Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Katsina United ta gayyaci ‘yan wasa 41 domin tantancewa

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

A shirye shiryen da ta ke yi na tunkarar gasar ƙwallon ƙafa na premier league ta ƙasa a kaka mai zuwa, ƙungiyar Katsina United ta gayyaci yan wasa 41 domin tantance wa.

Wannan bayanin ya fito daga babban sakatare a ma’aikatar wasannin da cigaban matasa Alhaji Muhammad Rabi’u lokacin da yake hira da manema labarai a Katsina.

Ya ce bayan kammala tantance waɗanda suka sami nasara, wasu daga cikin su za su kasance a ajin ƴan ƙasa da shekaru 23 da 25.

Babban sakataren ya hori ƴan wasan da aka gayyata da su zama masu nuna ɗa’a,ƙwazo da sadaukar da kai a tsawon lokacin da zasu yi wajen tantance wa.

A kakar da ta wuce ƙungiyar ta Katsina United ta kammala kakan wasan tana na 15 a teburin premier league ta ƙasa.

Masana harkar ƙwallon ƙafa a jihar na ganin yakamata gwamna Dikko Raɗɗa ya waiwayi ƙungiyar don ganin ya bata kulawar da ya kamata ko ta taɓuka wani abu a kakan wasa da za a shiga nan bada jimawa ba.

By ukarofi