Mataimakiyar Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi wa Dikko Raɗɗa ta’aziyar rashin Buhari

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Babban Sakataren yaɗa labarai na gwamnan, Muhammadu Kaula ya faɗi haka a wata sanarwa da ya aike wa manema labarai.

Mataimakiyar Hajiya Amina J Mohammed ta bayyana Muhammadu Buhari a matsayin mutum ne mai muhimmanci da shugabannin ƙasashen Duniya ke mutunta wa.

Hajiya Amina ta bayyana cewa halayyar sa riƙe gaskiya da riƙon amana da kuma bin doka da oda zai zama abin koyi dashi.

Tayi addu’ar Allah masa rahama sa mutuwa hutu ne a gare sa, “Allah ba iyalan sa da al’ummar Jihar Katsina da ƙasa baki ɗaya hakuri da juriya na rashi da aka yi.

A jawabinsa, gwamna Dikko Raɗɗa ya miƙa godiyar sa a madadin gwamnatin Jihar Katsina bisa wannan ziyarar da mataimakiyar sakataren ta kawo.

Ya bayyana ziyarar ta’aziyar da ta kawo da hakan ya nuna yadda marigayi Muhammadu Buhari ya ke da kuma a idanun duniya.

Haka kuma uwargidan shugaban ƙasa Oluremi Tinubu ta iso Katsina domin ziyarar ta’aziya ga iyalan marigayi Muhammadu Buhari.

Sauran waɗanda suka iso daga baya sun haɗa da tsohon shugaban majalisar Dattijai Bukola Saraki da tsohon gwamnan Kano kuma jagoran ɗarikar kwankwasiya Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.

By ukarofi