Zamfara: ‘Yan bindiga a babura sun halaka manoma tara da garkuwa da mutane 15

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wasu gungun ƴan bindiga a babura sun kashe manoma guda tara, kamar yadda wani jami’i da mazauna yankin da lamarin ya faru suka shaida.

Shaidun sun ce, ƴan bindigar sun kai farmaki ne a lokacin da wasu manoma suke tsaka da aiki a gonakinsu da ke waje da ƙauyen Jangebe dake Ƙaramar Hukumar Talatan-Mafara, inda suka kuma yi garkuwa da wasu mutane 15.

Sanannen al’amari ne a Nijeriya ƴan bindiga da ɓarayin daji sun addabi al’umma musamman waɗanda ke rayuwa a yankunan karkara, inda suke sanya wa wasu haraji yayin da suke garkuwa da mutane da kashe-kashen al’umma da babu dalili.

Wani mai suna Abubakar da ya sanar da manema labarai batun kuma ya halarci jana’izar mutane taran, ya ce ƴan bindigar ba su kira kowa ba akan waɗanda suka yi garkuwa da su.

Daga cikin waɗanda aka yi garkuwa da su akwai shugaban ƴan bijilante da na ƙasa da shi guda biyar da wasu mazauna yankin guda uku, sai wan mai suna Abu Zaki.

A shekarar 2021 ne aka yi garkuwa da ƴan mata sama da guda 300 da ke karatu a wata makarantar kwana a ƙauyen.

By Babaji