Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
Kalmomin da na yi amfani da su a matsayin taken rubutuna na wannan mako, na ɗauko su ne daga wata waƙar fitaccen mawaƙin siyasar nan Dauda Kahutu Rarara, Wanda ya yi wa marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari. Allah Ya jiƙan sa da rahama, Amin.
A yayin da nake wannan rubutu, marigayin na kwance a gidansa na gaskiya, inda aka binne shi a wani sashin na gidansa na wucin gadi da ke mahaifarsa a Daura ta Jihar Katsina. Mun ga yadda aka gudanar da jana’izar marigayin cikin dafifin dubban masoya da suka halarci jana’izar don yin bankwana da tsohon shugaban ƙasar, wanda da dama ke ganin ba a taɓa mutum mai farin jinin jama’a irin sa ba, a tarihin shugabannin ƙasar nan. Hakan kuwa na da nasaba da irin kyawawan halayensa na gudun duniya da yin komai cikin tsari da bin doka.
Na karanta a wani rubutu da wani ya yi yana mai cewa, Buhari ya tara ɗimbin jama’a masoya yana raye, kuma a bayan ransa ma ya ja zugar jama’a da aka daɗe ba a ga jana’iza irin tasa ba. Babu shakka wannan haka yake, a ’yan shekarun da na yi a duniya da nazarce-nazarce na ɗalibta, ban ga ɗan siyasar da jama’a suka nuna wa ƙauna ta tsakani da Allah, cikin shauƙin na nuna amincewa da yarda da ƙwarin gwiwa, kamar wannan bawan Allah ba.
Mutane sun sadaukar da rayuwar su da dukiyarsu da lokacin su, don dai su ga ya samu nasara ya karɓi madafun iko, don tabbatar da gaskiya da adalci, kamar yadda suke kyautata masa zato. Ni kaina a lokacin zaɓen 2015 na rasa wani ɗan uwana da ya faɗo daga kan babbar mota, lokacin da aka fita murnar samun nasarar zaɓen da ya yi. Bayan sa akwai wasu da dama da Allah Ya ɗauki ransu a sakamakon murnar da suka fita, ko kuma wani tsautsayi da ya same su ta dalilin taya tsohon shugaban ƙasa murna.
Duk da ƙalubalen da ’yan Nijeriya suka fuskanta a zango biyu na mulkinsa, inda har wasu suka riƙa ɗora alhakin hakan ga shi marigayin, da sauran maganganu iri-iri marasa daɗi, saboda tsananin da wasu tsare-tsaren gwamnatinsa suka haifar, bai hana mutane nuna alhini da jimami kan rasuwar sa ba. Mutane da dama sun zubar da hawaye, saboda rashin sa, sun kuma tausaya masa a matsayin mutumin da ya yi iyakar ƙoƙarin sa don kawo sauyi a ƙasar nan. Duk da kasancewar sa ɗan adam ajizi, kalaman sa na bayan cikar wa’adin mulkinsa, inda ya nemi gafarar ‘yan Nijeriya, kan kurakuran da aka samu, da halin da jama’a suka shiga, ya sa jama’a sun ƙara sallamawa al’amarin sa.
Yadda manyan shugabanni, sarakuna, da ‘yan siyasa daga ciki da wajen ƙasar nan, suka yi cincirindo a wajen jana’izar marigayin da masu karɓar makoki ya nuna irin girmamawa da suke nunawa shugaban, duk da ya bar duniya. Amma tasirin kyawawan halayensa a rayuwarsu, sun sa su jin nauyin cewa, akwai wani haƙƙi da ke kansu na kula da bayansa, kamar yadda ya kula da rayuwar su.
A yayin da duniya ke cigaba da alhinin rashin tsohon shugaban ƙasa, da faɗar kyawawan kalamai a game da halayensa na zahiri da suka sani, da kuma mu’amalar da suka yi da shi ta sirri, maganganu na ta bayyana daga wajen mutanen da suka samu kusanci da shi. Magana ta baya bayan nan ita ce wacce tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar LP, Peter Obi ya yi, inda yake cewa marigayin ya yi masa nasiha kan idan Allah Ya bashi mulkin Nijeriya ya tausayawa talakawan ƙasar nan. Hakan a cewarsa, ta ƙara tabbatar masa da cewa Buhari mutumin kirki ne, kuma yana da burin ganin ya kawo ƙarshen mummunan talauci da ke damun ’yan Nijeriya.
Shi kansa uban gayya, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, wanda jama’a da dama suka yaba masa saboda karamci da girmamawar da ya nuna wa gawar marigayin, daga lokacin da iyalinsa suka sanar da rasuwarsa, ya bayyana tsohon shugaban ƙasar a matsayin adalin shugaba, tsayayye, wanda ya gudanar da shugabanci nagari.
Mun kuma karanta wani rahoto da ke nuna cewa, Shugaban Bankin Duniya, Jim Yong Kim, ya bayyana cewa lokacin yana mulki tsohon shugaban ƙasa, marigayi Muhammadu Buhari ya buƙaci Bankin ya mayar da hankali wajen gudanar da ayyukan sa na Dala miliyan 200 da ƙungiyar raya ƙasashe ta IDA ta bayar don yankunan da rikice-rikice suka ɗaiɗaita a Arewa. Kodayake wannan rahoto ya haifar da ƙorafe-ƙorafe da dama daga ’yan Nijeriya da ke yankin kudancin ƙasar nan. Amma hakan bai hana wasu miliyoyin ’yan ƙasa yabawa da wannan ƙoƙari da ya yi ba, musamman ganin yadda tashe-tashen hankulan da aka fuskanta na Boko Haram ya lalata muhalli da zamantakewar jama’a a jihohin Borno, Adamawa da Yobe.
ƙungiyar Kare Haƙƙoƙin Musulmi ta Nijeriya, MURIC ta yabawa tsohon shugaban wanda ta kira shi da jagoran sabuwar Nijeriya, wanda ya gudanar da manyan ayyukan raya ƙasa a sassan ƙasar nan daban-daban. ƙungiyar ta ba da misali da aikin shimfiɗa titin dogo da aka yi tsakanin Legas zuwa Ibadan, da tsakanin Abuja zuwa Kaduna, da Itakpe zuwa Warri, waɗanda duk manyan ayyuka ne da za a daɗe ana cin moriyar su. MURIC ta tunatar da ’yan Nijeriya irin riƙon amana da kyakkyawan jagorancin da tsohon shugaban ƙasar ya nuna lokacin da ya riƙe PTF, Asusun Tallafin Manfetur. Ba tare da ya nuna rashin gaskiya ko cin amanar ƙasa ba.
’Yan Nijeriya da dama za su yi kewar marigayi Muhammadu Buhari a matsayin Shugaban ƙasar da ya yi mulki ba tare da ya arzuta kansa ba, bai saci dukiyar ƙasa ba, bai tara kuɗaɗe a bankunan ƙasashen waje ba, bai gina hamshaƙan gidaje ba. Bilhasali ma ya bar duniya da gidaje biyu ne kacal a matsayin abin da ya mallaka, da dabbobi ƙalilan. Ba shi da jiragen sama na ƙashin kansa, kuma ko abincin da yake ci ma ba wani abinci ne na hamshaƙan masu kuɗi ba. A bayyane yake cewa marigayi Muhammadu Buhari mutum ne mai gudun duniya, wanda bai damu da tara dukiya ko almubazzaranci da abin da ya mallaka da guminsa ba.
Mutane da dama na da ra’ayoyi daban-daban kan irin salon rayuwar marigayin. A wajen wasu, marigayi Buhari waliyi ne a cikin ’yan siyasa, wasu na yi masa kallon shugaba mai amana da gudun duniya, wasu kuwa na yi masa kallon matsolon shugaba wanda bai ci ba, kuma bai bari wasu sun ci ba! Akwai wasu da salon shugabancinsa ya sa suke yi masa kallon azzalumin shugaba marar tausayi, saboda ya ɗauki wasu matakan da ba su ji daɗin su ba. Wannan kuma dama hali ne na ɗan adam, ba kowa ne za ka yi wa daidai ba, kuma ba kowa be zai yaba maka ba. Kamar yadda ake cewa, daidan wani karkataccen wani. Mu dai muna yaba wa irin gudunmawar da ya bayar da halayensa na dattako da riƙon amanar sa da ta bayyana gare mu. Don haka muke ƙara faɗar, Ka fi su gaskiya, Baba!
Muna addu’ar Ubangiji Allah Ya jiƙan marigayi Muhammadu Buhari, kuma gafarta masa kurakuransa, Ya sa mutuwa ta zama hutu a gare shi.
