
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
An zartar wa shahararren jamrumin fina-finan Chana kuma mawaƙi, Zhang Yiyang hukuncin kisa bayan samun sa da laifin kashe budurwarsa mai ƙananan shekaru, lamarin da ya sa ya zama jamrumi na farko a Chana da aka taɓa yi irin haukuncin.
Wata kotun al’umma dake yankin Xianyang a Arewacin Shaanxi ta bayyana hakan a wani rahoton da ta fitar a watan Yuli, 2025.
Ta ce, an yi wa jarumin mai shekaru 32 hukuncin ne a ranar 18 ga watan Disambar 2024 bayan tabbatar da ya aikata laifin.
A shekarar 2022 ne Zhang ya daba wa budurwar tasa mai shekaru 16 wuƙa a sakamakon cacar baki da suka yi a tsakanin su, lamarin da ya sa ta yi ya zubar da jinin kana daga bisani ta rasu.
Bincike ya nuna cewa tun a 2021 ne suka soyayya, inda a lokacin da yarinyar ta nemi su rabu, sai mummunan iftila’in ya auku.
Daga bisani Zhang ya ɗauke wayarta bayan halaka ta inda ya haɗa da wuƙar da ya yi kisan tare da wasu ababen zargi ya watsar wani gulbi.
Bayan zurfafa bincike akan lamarin ne aka gano shi tare da zartar masa da hukuncin.
