An yi jana’izar Sarkin Gusau a masarautarsa

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

An yi jana’izar mai martaba Sarkin Gusau na 15 a Jihar Zamfara, Alhaji Ibrahim Bello a Gusau babban birnin Jihar Zamfara.

Da yake zantawa da manema labarai, shugaban majalisar sarakunan jihar, Sarkin Anka, Alhaji Attahiru Ahmed, ya bayyana cewa, kafin rasuwarsa, Sarkin Gusau ya bar wasiyyar cewa idan ya rasu a binne shi a maƙabartar gama garin al’umma dake garin Gusau ba a maƙabartar sarauta ba.

Sarkin na Anka, ya bayyana Marigayi Alhaji Ibrahim Bello a matsayin Musulmi mai kishin ƙasa wanda ya sadaukar da shekaru goma da yayi a kan karagar mulki ta hanyar taimakon al’ummarsa.

Alhaji Attahiru Ahmed ya cigaba da cewa, za a riƙa tunawa da shi bisa jajircewarsa na yaɗa addinin Musulunci da samar da zaman lafiya a jihar.

Shi ma da yake nasa jawabin, gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana rasuwar Sarkin Gusau Alhaji Ibrahim Bello a matsayin babban rashi ba ga iyalansa ba, masarautar Gusau, har ma da ɗaukacin al’ummar musulmi baki ɗaya.

“Mun yi rashin wani babban mutum Marigayi Alhaji Ibrahim Bello wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen yaɗa addinin Musulunci da ci gaban masarautarsa da kuma taimakon marasa galihu a lokacinsa”. In ji Gwamna Lawal

Taron jana’izar ya samu halartar dubban jama’a da suka haɗa da sarakunan gargajiya, malaman addinin musulunci, manyan jami’an gwamnatin jihar da dai sauransu.

By ukarofi