
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Al’umma a jihar Kano sun sanya alamar tambaya akan Kwamishinan Sufuri na jihar, Ibrahim Namadi bayan da ya yi lamuni ga wani shahararren dillalin miyagun ƙwayoyi mai suna Suleiman Ɗanwawu a kotu.
Ana tuhumar Ɗanwawu ne da laifuka takwas masu alaƙa da safarar ƙwayoyi, wanda Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) ta shigar akansa.
A ranar 16 ga watan Yuli ne aka bada belin sa a ƙarƙashin hukuncin Mai Shari’a M.S Shu’aibu na Babbar Kotun Kano.
A yayin haka ne Alƙalin ya sanya sharuɗɗa masu tsauri waɗanda daga ciki akwai ya nemo kwamishina daga cikin kwamishinonin gwamnatin jihar wanda zai tsaya masa sannan kuma zai ajiye Naira miliyan 5 a kotun.
A wani yanayi na ban mamaki ne Kwamishina Namadi ya cike sharaɗɗin lamunin a wata takarda da ke ɗauke da kwanan wata kamar haka; 18 ga Yuli, inda a ciki ya nemi zama wanda zai tsaya wa Ɗanwawu.
Tun a ranar 28 ga watan Mayu ne aka gurfanar da Ɗanwawu kana daga bisani aka ajiye shi a hannun hukuma har zuwa lokacin belin nasa.
