Ɗangote ya yi murabus a kamfanin simintinsa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shahararren Attajirin ɗan kasuwan nan a Nijeriya da Nahiyar Afirka, Alhaji Aliko Ɗangote, ya yi murabus daga matsayinsa a Kamfanin Simintinsa na ‘Dangote Cement’, kamar yadda wani rahoto da The Eagle ta fitar a ranar Juma’a ya bayyana.

Gabannin haka, Ɗangote ya yi aiki a kamfanin, wanda rukuni ne daga rukunan babban kamfaninsa a matsayin ɗaya daga cikin jagorori da kuma zama shugaba.

Rahoton ya kuma bayyana cewa wani jami’i mai suna Emmanuel Ikazoboho ne wanda zai maye gurbin hamshaƙin attajirin a muƙamin da ya barin.

Tun a watan Yunin shekarar nan ne Ɗangote ya yi murabus daga rukunin simintin kasuwancinsa.

Wasu rahotanni sun tabbatar da cewa tun a 12 ga Yuni, 2025 ne Ɗangote ya yi murabus a matsayin Shugaban tawagar daraktoci na kamfanin tace suga, wato ‘Dangote Sugar Refinary PLC’.

Lamarin da ya kawo ƙarshen zamansa a matsayin na tsawon shekaru 20, kamar yadda Sakataren matatar, Temitope Hassan ya tabbatar a wata sanarwa.

By Babaji