Daga ABDULLAHI HASSAN YARIMA
Dan abokina ne. Sau huɗu zuwa sau biyar a lokuta daban-daban na je na ɗauko yaron bayan an tashe su daga makaranta. Watarana na je na ɗauko shi sai na biya wani kanti na siya masa biskit. Na tambaye shi da ya lissafa adadin ‘yan gidansu na siya musu tare. Ya faɗi sunayen su amma kuma ya kasa simple arithmetic kamar bakwai a tara da biyu. Sai da ya ɗan sha wahala kafin ya iya ba ni amsa.
“Slow learner ne.” Mahaifinsa yace da ni bayan da na ba shi labari. Na yarda da hakan, sai dai na kula yaron na da wani ƙuality na musamman.
Burina mahaifinsa ya fahimci hakan, kuma ya gano a ranar juma’ar da ta gabata bayan an idar da sallah. Yaron ya gaisa da wani maƙocinsu da aka yiwa rasuwa kwanaki kaɗan da suka gabata. Ga mamakin uban sai ya ji ɗan na ce da wancan wanda aka yiwa rasuwar ya ƙarin haƙuri? Saboda yana ganin ƙanƙantar yaron da har ya iya tunawa kuma ya yi wannan azancin na yin gaisuwa batare da ya ji wani a kusa da shi ya yi ba.
Lokacin da ya ba ni wannan labarin sai na tuna masa da abinda ya faru a lokacin da na taɓa siya masa biskit shi da ‘yan uwansa. A lokacin har na cewa mai kantin ya ba ni wata alawa da na san matata ta na so. Sai kuma na fasa.
“Me ya sa ka fasa siya mata?” Arfat ya tambaye ni bayan da na faɗa masa da matata na yi niyyar siyawa.
“Na tuna ba ta nan.” Na ba shi amsa.
“Ba sai ka ajiye mata ba, idan ta dawo ka ba ta.” Shi ya yi conɓincing ɗi na na siya mata alawar. Tun kafin ta sha alawar na faɗa mata credit ɗin na Arfat ne. Sai ta ji yaron ya ƙara shiga ranta.
Wannan na daga cikin abinda ba mu cika lura da shi ba tun daga cikin gida har zuwa makaranta game da rayuwar ‘ya’yanmu.
A makaranta an fi koyar da competition fiye da compassion. Iyaye ma sun fi damuwa da su ji yaronsu ya zo na ɗaya ko ace ya fi kowa gane karatu a aji. Amma mu na da ƙarancin kula da emotional world ɗin su. Ya yanayin tausayi da jin ƙai? Ya yanayin shaƙuwarsa da ‘yan uwansa? Ya alaƙarsa ta ke da wani wanda ya ga ya na cikin wani mawuyacin hali? Zai ji tausayinsa? Zai ƙyamace shi? Ko kuma dariya zai yi masa? Ya yake responding idan zai fita ya ji ƙanwarsa ta fashe da kuka kan ta na so ta bi shi su fita tare? Ya na jan ta su tafi tare ko kuma kawai tafiyarsa yake yi shi kaɗai? Ya na iya sadaukar da wani abu na ɗan lokaci don ƙaninsa ya ji daɗi?
A kwanakin baya lokacin da ƙaramin ɗa na Muhammad ba lafiya aka je asibiti ana neman jijiya a jikinsa an rasa. Ana ta ɓuɓɓula masa jiki da allura yana ihu. Yayansa Ahmad na wajen sai shi ma kawai ya fashe da kuka. Da aka ba ni labari na ji daɗin hakan. Ban kalli abinda ya yi a matsayin dolantaka ba, na kalli abin a matsayin soyayya da shaƙuwa. Physically ba shi ake tsirawa allurar ba, amma psychologically ya na jin zafin allurar a ransa. What a loɓe?
Shi ma Muhammad wancan satin ya yi wani abu da ya burge ni. Da daddare na ɗauke shi muka je muka siyo gurasa. Mu na dawo wa muka tarar Ahmad ya yi bacci. Na ce kuma ba za a tashe shi ba.
“Sai a ajiye mi shi na shi sai da safe.” Inji Muhammad. Na fi jin daɗin maganar nan da ɗan shekara uku ya faɗa fiye da gurasar da muka siyo.
A cikin wani littafi da ba ta kammala ba wanda ya ƙunshi hanyoyin da ake bi wajen tarbiyya Safiyyah Jibril Abubakar na cewa “Iyayen da ke son cigaban kan su ne ke samar da ‘ya’ya ma su son cigaba.” A cikin littafin ƙarƙashin wani babi da ta kira da suna ‘Kyautayi da Shaƙuwa’ marubuciyar na cewa “Ku zama ɗaliban ‘ya’yanku ta hanyar nutsuwa da fahimtar yadda suke nazartar rayuwa, ta haka ne za ku fahimci a wajen da suke da rauni ku tallafe su, sannan ku gane wajen da suke da ƙwazo ku ƙarfafa musu gwuiwa.”
Gani ya kori ji. Wani babi ne mai zaman kan sa a cikin littafin. Inda marubuciyar ta yi bayanin cewa duk irin abinda kake so yaro ya yi saurin koya to sai ka na aikatawa a gabansa ya na gani.
Sai dai kuma babban abinda zai cigaba da kawo mana cikas a wannan zamanin iyaye ba su da lokacin ‘ya’yansu. Duk an tattara komai an bar wa malamai. Dayawa malamai sun fi sanin hali da yanayin da yara ke ciki fiye da iyayensu.
It is good mu gane cewa ba karatu kawai ake buƙata ba, akwai wasu abubuwa da su ne ɗan adam ke tafiyar da rayuwa. Su ne abubuwan da ke bambanta ɗan adam da machine. Wato Emotional Engagement.
Wataƙila da ace Robert j Oppenheimer tun ya na yaro an koya masa kyautayi soyayya da jin ƙai, da ba lalle ne ya jagoranci haɗa makamin ƙare dangi da ƙasar Amurka ta yi amfani da su a kan ƙasar Japan a yaƙin duniya na biyu ba.
Jarrabawar ƙarshen zangon karatu na ƙarato wa. Da ba don ƙaramin yaro ba ne, da sai na yi hasashen wataƙila yanzu gaban Arfat na faɗuwa, tun da ba a bayar da maki kan abinda ya fi ƙwarewa a kai. To wa ya ma ya damu da wannan fagen?
Abdullahi Yarima, marubuci ne a Kano, ya wallafa rubutun nan ne a shafinsa na Facebook
