Gwamnatin Katsina ta koka kan yadda ake yaɗa labaran ƙarya kan ta’addanci a jihar

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnatin Jihar Katsina ta lura da damuwa irin yadda wasu mutane ke ƙoƙarin haifar da tsoro da firgici ga al’ummar jihar ta hanyar yaɗa labaran ƙarya da na ɓatanci a shafukan sada zumunta.

Wannan bayanin ya fito ne daga bakin kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro Dr Nasiru Mu’azu Ɗanmusa a wata takardar sanarwa da aka rabawa manema labarai a Katsina.

Ya ce waɗannan labarai ana yin su ne don rage muhimmin ci gaban da aka samu a yaƙin da ake yi da ‘yan bindiga da rashin tsaro a ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dikko Raɗɗa.

Dr Ɗanmusa ya bayyana cewa lokacin da gwamna Raɗɗa ya hau mulki a shekarar 2023, dukkanin ƙananan hukumomi 34 na jihar suna fama da matsalar ‘yan bindiga. “A yau, tare da dabarun da aka mai da hankali kan su da haɓaka haɗin gwiwa da hukumomin tsaro, an samu gagarumin ci gaba a yawancin sassan jihar,”ya ce.

Ƙananan hukumomin da suka tsira daga hare-haren ‘yan bindigan sun haɗa da
Jibia, Batsari, Ɗanmusa, Katsina, Ɓatagarawa, Charanchi, Bindawa, Ingawa, Ƙafur, Ɗanja, Kusada a cewar kwamishinan.

Haka kuma ya bayyana yankunan da suka inganta da Kuma waɗanda ke da ɓatattun matsalolin tsaro sun haɗa da
Malumfashi, Kurfi, Dutsinma, Kankia, Musawa, Bakori, Funtua, Sabuwa, Dandume.

Sai yankunan da har yanzu suke fama da hare-hare wanda gwamnati na bakin ƙoƙarin ta wajen magance matsalar sune,
Faskari, Ƙanƙara, Safana, Matazu inji Dr Ɗanmusa.

Kamar yadda kwamishinan ya faɗa duk da ƙalubale da ake ci gaba da fuskanta a wasu ƙananan hukumomi, “Gwamna Raɗɗa ya ci gaba da jajircewa wajen dawo da zaman lafiya da tsari,”ya ce.

“Ko da a lokacin hatsarin da ya samu kwanan nan da kuma lokacin da yake murmurewa, bai taɓa daina tattaunawa da manyan masu ruwa da tsaki ba, inda yake karɓar rahotannin tsaro na yau da kullum daga manyan jami’an tsaro da sauran manyan masu ruwa da tsaki,”kwamishinan ya bayyana haka.

Sai dai kwamishinan ya nuna takaici da kan yadda wasu muryoyi a shafukan sada zumunta, maimakon su goyi bayan waɗannan ƙoƙarin, sai su ci gaba da yaɗa labaran ƙarya don samun nasarar buƙatar kan su.

Kwamishinan ya tunatar da al’ummar jihar cewa yaƙin da ake yi da ‘yan bindiga abu ne mai sarƙaƙiya. Yawancin hare-haren suna faruwa ne a cikin dazuzzuka masu zurfi, inda ayyukan mayar da martani ke buƙatar lokaci, haɗin gwiwa, da kuma bayanan sirri na gida.

“Shi ya sa aka kafa Katsina Community Watch Corps don taimakawa a waɗannan yankuna masu wuya kuma suna aiki kafaɗa da kafaɗa da sauran jami’an tsaro,”inji Ɗanmusa.

Ya sanar da cewa ya zuwa yanzu jami’an tsaron CWC fiye da 100’aka kashe,yan sanda 30 da wasu sojoji a yayin da suke gudanar da aikin su.

Ya jaddada ƙudirin gwamnatin jihar na ci gaba da kashe kuɗi masu yawa don tabbatar da cewa jami’an tsaro suna da kayan aiki masu kyau da kuma ƙarfafawa.

Domin haka kwamishinan ya nemi goyon bayan al’ummar jihar wajen bada tasu gudunmawa a ƙoƙarin da gwamnatin keyi na kawar da ta’addanci a jihar.

Ya shawarci al’ummar Katsina su kuma guje wa jaraba imani ko yaɗa labaran da ba a tabbatar da ingancin shi ba.

By ukarofi