Wani abu da ya kamata a sani game da cutar hawan jini

Spread the love

Tare da CHIROMA AMINU ASID

Cutar hawan Jini:

Menene Hawan Jini? Hawan jini shine buguwar zuciya ya wuce adadin da ake buƙata a jikin mutum. Hawan jini na ɗaya daga cikin cututtuka masu haifar da illoli a jiki. Daga ciki har da rasa rai. Yana kashewa nan take.

A ƙa’ida fa, cutar hawan jini kashi 85% ba a san abunda ke haddasa shi ba.

Yanayin  hawan jini:

Alamomin da za a fahimci akwai alamun hawan jini sun sha bamban da illolin da yake haifarwa.

Hawan jini yana zubar da ciki, ya tsotse jini, ya haddasa tsinkau, ya sa ciwon sashe da ma rasa rai.

Mai cutar hawan jini zai iya zama da illolin da hawan jininsa ya haddasa masa ko da kuwa an warke daga hawan jinin.

Rashin ji, rashin gani da karkacewar baki ko karyewar harshe na daga cikin sauran illolin hawan jini.

Alamomiin hawan jini:

A ƙa’ida ta hawan jini, ba a tabbatar da shi ga wani sai da abun awonsa, alamominsa kaɗai ba sa tabbatar da shi.

Faɗuwar gaba, zafin ƙirji, rashin bacci, kumburin ƙafafu ko jiki, ciwon kai da hauhawar bugun zuciya na daga cikin alamominsa.

Matakar sauke hawan jini:

Matakai biyu waɗanda ke saurin saukar da hawan jini su ne a yi ta yin fitsari nan take, sannan a bar cin gishiri. Rashin yin fitsari na daga cikin ababen da ke ta’azzara matsalar hawan jini.

Kamuwa da hawan jini:

Cutar hawan jini tana daga cikin cututtukan da ake gado daga uwaye da kakanni, amma ba lallai kowa ya samu matsalar ba.

By ukarofi