Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
A wani babban yunƙuri na yaƙi da cutar zazzaɓin cizon sauro a faɗin jiha.An ƙaddamar da magunguna da gidan sauro a fadar hakimin Mashi da ke garin Mashi.
Gwamnan Katsina, Malam Dikko Raɗɗa, wanda ya samu wakilcin Kwamishinan Lafiya , Hon. Musa Adamu Funtua, ya bayyana gamsuwarsa da irin yadda ake ci gaba da ƙoƙari wajen daƙile cutar a sassa daban-daban na jihar.
Gwamnan ya kuma yabawa ƙoƙarin gwamnatin sa wajen inganta lafiyar al’umma da kare dukiyoyinsu.
Shugaban ƙaramar hukumar Mashi, Hon. Salisu Kallah, a jawabinsa na maraba, ya nuna farin cikinsa bisa yadda aka zaɓi ƙaramar hukumar su a matsayin inda aka fara rabon gidan sauro. Ya kuma godewa Gwamna Raɗɗa bisa irin ayyukan raya ƙasa da yake aiwatarwa a yankin.
Taron ya samu halartar wakilai daga sassa daban-daban na jihar, ciki har da Iyan Katsina, wanda shi ne wakilin Sarkin Katsina a wajen taron, da sauran manyan masu ruwa da tsaki a fannin lafiya da walwalar jama’a.
Fatan da mutane keyi shine magungunan da gidan sauron ya isa kowane lungu na faɗin jihar ganin yadda cutar ta karaɗe jihar.
