Ambaliyar ruwa ta sake mamaye Maiduguri

Spread the love

Daga MUHAMMAD AL-AMIN a Maiduguri

Wani ruwan sama mai kama da bakin-ƙwarya, wanda ya ɗauki sama da awanni uku ya na sauka a birnin Maiduguri, babban birnin Jihar Borno, yayin da hakan ya jawo ambaliyar ruwa, wanda ya tilasta jama’a da dama a wasu unguwanni ƙauracewa matsugunansu.

Wasu daga cikin unguwannin da al’amarin ya fi shafa sun haɗa da Damboa road, Moduganari, Ngomari, haɗi da wasu sassa a birnin, wanda sakamakon haka su ka bar gidajensu tare da neman mafaka a gidajen dangi da abokai.

Wani mazaunin unguwar Damboa Road; bayan gidan Indimi, ya bayyana cewa suna cikin fargabar yuwuwar sake shiga cikin mawuyacin halin ambaliyar ruwan da suka fuskanta a baya.

Ya ce, “Kwann baya abin ya fara ne kadan-kadan, amma yau da safe samun mamakom ruwa, kamar da bakin ƙwarya, abin yayi tsananin da ya jawo ambaliyar ruwa.” In ji shi.

A Moduganari kuma, Mista Joshua Solomon, ya tabbatar da cewa, gidaje masu yawa ne suka rushe a unguwar.

“Idan ka kula ga wasu gidaje can a gefe, ruwa ya shiga kuma ina da tabbacin masu gidan sun fice zuwa neman mafaka. Ga namu gidan nan, shima ruwan ya tunkaro shi. Kusan haka abin yake a wannan unguwa.”

Har wala yau kuma, wani jami’in gwamnatin Jihar Borno ya shaida wa wakilinmu cewa, ambaliyar ruwan ta rutsa da cibiyar kula da kiwon lafiya a matakin farko da ke gundunar Ngomari a Maiduguri.

Ya ƙara da cewa, “Hukumar UNICEF tare da haɗin gwiwar hukumar lafiya a matakin farko ta Jihar Borno sun shirya ƙaddamar da aiwatar da matakin magance matsalolin da ka iya biyo bayan ambaliyar ruwan, a ƙaramar hukumar Jere.”

Wannan ambaliyar ta na zuwa ne bayan makamanciyarta wadda ta afku watanni 10 da suka gabata, a birnin Maiduguri da kewaye, inda mutane da dama suka rasa rayukansu, sa’ilin da wasu dubbai suka rasa matsugunansu.

Mazauna yankin da masu ababen hawa na kira da a ɗauki mataki cikin gaggawa domin daƙile matsalolin da ambaliyar ruwan za ta jawo a birnin na Maiduguri.

By ukarofi