ZAWFOG ta ƙaddamar da kamfen na shuka bishiyoyi da jan kunnen al’umma kan sare itatuwa

Spread the love

Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe

Gidauniyar Zakka da Waqf ta Jihar Gombe (ZAWFOG) ta ƙara azama wajen yaƙi da sare bishiyoyi ba bisa ƙa’ida ba, inda ta ƙaddamar da kamfen na shuka bishiyoyi karo na bakwai a ƙauyen Majidadi, ƙaramar hukumar Shongom.

Shugaban gidauniyar, Dakta Abdullahi Abubakar Lamido, ya bayyana sare bishiyoyi ba tare da sake dasu ba a matsayin “mummunar ɓarna ga muhalli” wadda ke haifar da ambaliya, zaizayar ƙasa da sauyin yanayi.

“Sare bishiya ba tare da sake shuka ba, laifi ne ga halittar Allah. Musulunci ya koyar da mu mu kula da muhalli, kuma kowace bishiya da mutum ya shuka tana zama sadaka mai ɗorewa da za ta ci gaba da kawo lada har bayan mutuwarsa,” in ji shi.

A wannan shekara, ZAWFOG za ta raba dubban tsirrai kyauta ciki har da mangwaro, gwaiba, zogale da sauran su ga gidaje, makarantu, masallatai da wuraren jama’a a ƙananan hukumomi takwas da suka ci gajiyar shirin tun farko.

Hakimin Majidadi, Alhaji Adamu Madugu, ya yaba da wannan shiri tare da sanar da sabbin dokokin gari da za su tilasta wa duk wanda ya sare bishiya ya dasa guda biyu a madadinta.

“Duk wanda ya sare bishiya zai dasa guda biyu. Duk wanda ya yi sakaci da tsiron da aka ba shi, to yana cutar da ci gaban al’ummar mu,” in ji shi.

Kamfen ɗin ya haɗa da wa’azin mako-mako a masallatai, laccoci ga jama’a, dasa bishiyoyi a makarantu, asibitoci da wuraren ibada, da kuma shirye-shiryen wayar da kan jama’a a gidajen rediyo da talabijin, domin ƙarfafa shuka bishiyoyi cikin tsari da kare muhalli daga lalacewa.

By ukarofi