
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar kula da Ƴancin Haƙƙin Mallaka ta Ƙasa (NCC) da haɗin-gwiwar Ƙungiyar Rajistan Intanet ta Ƙasa (NiRA) da Cibiyar Rajista ta Ƙasa, ta dakatar da manhajar bidiyoyin fina-finai na MovieBox bisa yaɗa fina-finai, waƙoƙi, wasannin kai-tsaye daga Nijeriya da wajenta ba tare da izini ba.
Ƙungiyoyin ƴancin mallaka na masana’antun harkar fina-finai da makamantansu sun yaba da hukunci, duba da yadda hukumomin da lamarin ya shafa a Nijeriya ke ɗaukar matakan da suka dace kan ƴancin haƙƙin mallaka.
A wani rahoto da NCC ta fitar, ta bayyana haramtattun ayyukan manhajar a matsayin abinda ke daƙile ayyukan kula da haƙƙin mallaka a yanar gizo ga hukumomi.
Rahoton ya bayyana yadda sashin yanar gizo na manhajar ke kutse ga ayyukan da aka taƙaice wuraren haska su sakamakon rashin kiyaye ƴancin haƙƙin mallaka.
Akan haka ne hukumar ta yaba wa NiRA bisa yadda ta gaggauta ankarar da hukumomin da suke da alhakin dakatar da hakan musamman sashin yanar gizo masu samar da sabis wajen toshe ayyukan da ba a amince da su ba.
