Kotun ƙasar Sin ta rataye jarumi Zhang Yiyang kan kisan budurwarsa

Spread the love

Daga AISHA ASAS 

Wani hukunci mai ɗaukar hankali ya sauka a masana’antar nishadin ƙasar Sin, bayan da aka tabbatar da kisan gilla da Zhang Yiyang, fitaccen jarumi kuma mawaƙi, ya yi wa ƙaramar budurwarsa. Hukumar shari’a ta ƙasar ta tabbatar da zartas da hukuncin kisa a kansa.

Zhang, mai shekaru 32, ya halaka budurwarsa mai shekaru 16 a cikin 2022 bayan wata gardama da ta shiga tsakaninsu. Hukumar shari’a ta bayyana cewa, ya sare jijiyoyin wuyanta da wuka, wanda ya janyo zubar jini sosai har ta rasa ranta.

Binciken ‘yan sanda ya nuna cewa, suna tare tun 2021, amma matar ta nuna alamar son kawo ƙarshen dangantakar, lamarin da ya janyo rikici mai muni. Bayan kisan, Zhang ya ɓoye wayar mamaciyar da wasu abubuwa da suka nuna laifinsa a tafkin ruwa, sannan ya yi yunƙurin kashe kansa a wani otal.

Daga baya jami’an tsaro suka kama shi, kuma aka gurfanar da shi. Hukuncin da aka zartar masa a Disamba 2024 yanzu ne aka bayyana shi a hukumance.

Zhang ya shahara da waƙoƙi kamar “I Only Care About People Who Care About Me”, amma yanzu an jefa shi cikin tarihin baƙar fata na masu laifi a fagen nishadi a Asiya.

By ukarofi