NOLLYWOOD: Kazamin rikici ya sake ɓarkewa tsakanin Iyabo Ojo da Lizzy Anjorin

Spread the love

Daga AISHA ASAS 

An sake kunna wutar rigima tsakanin fitattun jaruman Nollywood guda biyu, Lizzy Anjorin da Iyabo Ojo, bayan sanarwar cewa, Priscilla Ojo, ‘yar Iyabo, na ɗauke da juna biyu daga shahararren mawaƙin Tanzaniya, Juma Juɗ.

Sanarwar ta fito ne a Instagram inda Priscilla ta saki hotunan ciki, tare da saƙonnin jin daɗi daga masharhanta da masoya. Sai dai shiru da Lizzy Anjorin ta yi kan lamarin ya janyo zargi daga jama’a, wanda ya sake tayar da rikicin da ke tsakaninta da Iyabo tun da daɗewa.

Anjorin ta mayar da martani cikin wata faifan bidiyo mai zafi, inda ta caccaki Iyabo da iyalinta, tana mai kare kanta bisa zargin ƙiyayya da nuna bambanci. Sai dai kalamanta masu zafi da suka shafi Priscilla sun fusata jama’a, har suka mayar da martani cikin fushi.

Jaruma Iyabo Ojo ta ce, ko da tana son zaman lafiya, ba za ta lamunci barazana ko ɓatanci da ya shafi ‘ya’yanta ba. Ta jaddada cewa, “Idan wani abu ya same ni ko ‘ya’yana, Lizzy ce ke da laifi.”

Masu kallo da mabiyan Nollywood na kira da a daina yayata rigima, tare da buƙatar a sasanta lamarin cikin ruwan sanyi.

By ukarofi