Daga AISHA ASAS
Shahararren mawaƙin nan na Kannywood, Hamisu Breaker, tare da jarumin TikTok, Abubakar Ibrahim, wanda aka fi sani da Al-Amin G. Fresh, sun shiga hannun hukuma bayan da Kotun Tarayya a Kano ta same su da laifi kan cin zarafin takardun Naira.
Kotun ta yanke musu hukuncin ɗaurin wata biyar a gidan kurkuku ko kuma zaɓin biyan tara ta Naira 200,000 ga kowannensu.
Hukumar Yaƙi da Rashawa da Zagon ƙasa ga Tattalin Arzikin ƙasa (EFCC) ce ta gurfanar da su a gaban Mai Shari’a Sale Musa Shuaibu, inda kowannensu ya amsa laifin watsar da takardun kuɗin Naira a bainar jama’a.
A cewar hukumar, Hamisu Breaker ya watsa takardun Naira 200 da ya kai kimamin Naira 30,000 a wani biki da aka gudanar a Hadejia da ke Jihar Jigawa, yayin da G. Fresh kuwa, an kama shi da watsar da ‘yan Naira 1,000 a bikin buɗe wani shago a unguwar Tarauni da ke Kano.
Alƙalin kotun ya yanke musu hukunci, tare da gargaɗin jama’a da su guji irin wannan saɓa wa doka. Hukumar EFCC ta jaddada cewa, tana da ƙwarin gwiwar kawar da duk wani amfani da kuɗi da ya saɓa wa doka komai girman mutum.
