
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A wani yunƙuri na garambawul ga harkokin jagorancin jami’o’in tarayya, Shugaba Bola Tinubu ya amince da cire Dakta Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin shugaban majalisar jagorancin Jami’ar Bayero ta Kano (BUK).
Ya kuma maye gurbinsa da AVM Sadiq Ismail Kaita (mai ritaya) a muƙamin.
A wata sanarwa da Kakakin shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya fitar, ranar Juma’a, ya ce an yi haka ne da nufin bai wa Gawuna damar mayar da hankali akan aikinsa na shugaban Hukumar Gine-gine ta Tarayya (FHA), ƙarƙashin Ma’aikatar Gine-gine da Raya Birane.
Gabannin ya yi rataya, AVM Kaita ya yi aiki a matsayin Daraktan kula da ɓangaren dabarun ayyuka a Hedikwatar Tsaro (DHQ) sannan daga bisani a matsayin shugaban ci-gaban sauye-sauye da ƙirƙira a rundunar sojojin Nijeriya.
A matsayinsa na tsohon soja, ana sa ran zai samar da tsarin inganta harkokin jagorancin jami’ar ta fuskar horo da kyawawan sauye-sauye a yayin da jami’o’in ƙasar ke fuskantar matsi akan lamuran ababen more rayuwa, kuɗi da gogayya a mataki na duniya.
Jami’ar Bayero ɗaya ce daga cikin manyan jami’o’in Arewacin Nijeriya duba da yadda ta zama fagen bincike, tattaunawa kan harkokin ci-gaba tsakanin masu ruwa da tsaki da zamanantar da harkokinta a shiyyar.
