Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Gwamnatin Jihar Zamfara ta jaddada kudirinta na kyautata jin daɗin masu yiwa ƙasa hidima da kuma tsaron lafiyar su a lokacin da suke a jihar.
Gwamnan jihar, Dauda Lawal ya bayyana haka a wajen bikin rantsar da masu yiwa ƙasa hidimar watau Batch B Stream I na shekarar 2025 da aka tura jihar, wanda aka gudanar a sansanin NYSC Orientation Camp, dake a Gusau yau Juma’a.
Gwamnan wanda ya samu wakilcin babban sakatare a ma’aikatar matasa da wasanni Alhaji Nasiru Galadima Kaura, ya bayyana cewa sake biyan alawus alawus ga masu yiwa ƙasa hidimar na daga cikin alƙawuran da ya ɗauka na inganta jin daɗin su.
Dokta Lawal ya buƙaci ’yan ƙungiyar da su sanya kishin ƙasa, gaskiya da riƙon amana a yayin bautar ƙasar da aka turo su suyi a jihar .
Da yake jaddada ƙudirin gwamnatinsa na tabbatar da tsaron lafiyarsu, gwamnan ya bayyana cewa, “Kiyaye walwalar kowane ɗan bautar ƙasa shi ne mafi muhimmanci ga gwamnati sa.
“Zamu jajirce sosai wajen tabbatar da tsaron ku a tsawon shekarar hidimar ƙasa da za kuyi, baya ga samar da yanayin da zai ba ku damar yin fice don kammalawa cikin nasara”
A nasa jawabin, kodinetan NYSC reshen Jihar Zamfara, Mallam Muhammad Lawan Ahmed, ya bayyana cewa, za a gudanar da atisayen na tsawon makwanni uku, wanda zai hada da laccoci kan al’adun jihar, da horon motsa jiki, bunƙasar shugabanci, da shirye-shiryen koyon sana’o’i da dai sauransu.
Ya kuma ja hankalin ‘yan bautawa ƙasar dasu ɗauki horon da muhimmanci, inda ya jaddada muhimmancinsa ga ci gabansu da kuma samun nasarar shekarar hidimarsu.
Ko’odinetan jihar ya kuma yabawa Gwamna Lawal bisa irin goyon bayan da gwamnatin sa ta ba shi, musamman yadda aka dawo da alawus-alawus na matakin jiha ga ‘yan bautar ƙasa bayan wani dogon lokaci da aka dakatar dashi.
Ya kuma yi kira da a samar da wani katon wurin da za a kafa sansanin ‘Orientation Camp’ domin ɗaukar ƙarin yawan ‘yan bautawa ƙasa da ake aikawa a jihar ta Zamfara.
Hakazalika an ratsar da jimillar masu yiwa Kasa hidimar su 554 a wajen bikin da babban alƙalin Jihar Zamfara, wanda ya samu wakilcin Aishatu Jibrin, mataimakiyar magatakardar babban kotun jihar Zamfara ta gudanar.
