Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
A wata sanarwa ɗauke da sa hannun jami’in hulɗa da jama’a na ƙungiyar, malam Nasiru Gide ya ce sayen ƴan wasan zai ƙarawa ƙungiyar ƙarfin tunkarar kakan wasan da za a shiga.
Nasiru Gide ya na mai tabbacin cewa da wannan sabbin ƴan wasa, Katsina United za ta taka rawar gani a gasar Firimiya ta ƙasa.
Sabin yan wasan sun haɗa da Adekunle Oluwasegun daga kwara United sai Philip Clement Oguche daga Abia warriors da wasu cikinsu daga Bendel United.
Sai ta ɗauki Moses daga Enugu Rangers da Falotu Azeez Al’amuran daga Alnasar Zlitan na kasar Libiya da Innocent Segun na Sunshine.
Shugaban ƙungiyar ƙwallon kafar Alhaji Surajo Umar Ɗalibi ya jagoranci sanya hannu a yarjejeniyar tsakanin hukumar gudanarwar na ƙungiyar da sabbin ƴan wasan.
