An ƙona mashin ɗin masu ƙwacen waya a Kano

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

An ƙona mashin mai ƙafa uku wato a daidaita sahu wanda ake zargin na masu ƙwacen waya ne, ya yin da su kuma aka garzaya da su ofishin ƴan sanda da ke Goron Dutse.

Lamarin ya faru ne a kusa da gidan man ALIKO da ke kan titin Goron Dutse kwanar Taya da ke Kano.

Shaidun gani da ido sun shaidawa Blueprint Manhaja cewa, ɓarayin bayan cin duka da su ka yi an yayyaga masu riga, sannan aka garzaya da su ofishin ƴan sanda da ke yankin.

By ukarofi