Nuna fin ƙarfi ne rufe gidan rediyo – Amnesty ga Gwamna Bago

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ƙungiyar kare ƴancin ɗan-adam (Amnesty International) ta soki rufe gidan rediyon Badeggi mai mita 90.1 zangon FM da ke Minna, Babban Birnin Neja da Gwamna Umar Bago na jihar ya yi, lamarin da a cewarta tauye haƙƙi ne ga ƴancin gudanar da gidajen jaridu acikina l’umma.

A ranar Alhamis gwamnan ya umarci a rufe gidan rediyon a lokacin da jiga-jigan ƴan jam’iyyar APC ke gudanar da babban zama a gidan gwamnatin jihar, inda ya zargi shirye-shiryen da gidan rediyon ke yaɗawa da haifar da rikici da nuna rashin ƙwarewa.

Da ya ke jawabi a ranar Asabar, Daraktan ƙungiyar a Nijeriya, Isa Sanusi ya ce umarnin ba shi da goyon bayan shari’a, sannan danniya ce ga aikin jarida.

Ya ce, Amnesty International ta yi alla-wadai da matakin gwamnan duba da cewa gidan rediyon zaman kansa ya ke ba ƙarƙashin gwamnati ba.

Sanusi ya bayyana cewa, hakan ya saɓa ƙa’idodin jagoranci wanda acewarsa rashin adalci ne, yana mai cewa a dokar ƙasa ma gwamnoni ba su da ikon rufe gidajen rediyo.

Ya kuma yi kira ga gwamnatin jihar da ta gaggauta buɗe gidan rediyon domin ya koma cigaba da aikinsa.

Kazalika, ya soki gwamnatin wajen kai wa gidajen jaridu hari a yayin da rashin tsaro ke ƙara dabaibaye sassan jihar inda ake cigaba da kashe-kashen mutane a ƙauyuka.

By Babaji