Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
A wani mataki na sauƙaƙa tsadar kayan abinci, masu kiwon kaji a jihar Legas sun bayyana shirin rage farashin kwai ta hanyar sayar da shi kai tsaye ga masu saye a faɗin ƙananan hukumomi.
ƙungiyar Masu Kiwon Kaji ta Nijeriya (PAN) reshen Legas ta bayyana cewa shirin na da nufin kawar da baba-keren ’yan kasuwar tsakiya da ke janyo hauhawa farashin kayayyaki, wanda hakan ya sa ƙwai ke yin tsada.
A halin yanzu, masu saye da sayarwa su na biyan N6,500 a kowane kiret, duk da cewa farashin sari na tsakanin N5,000 zuwa 5,500.
Domin ɗinke wannan giɓin, PAN na haɗa gwiwa da hukumomin ƙananan hukumomi don kafa wuraren sayar da ƙwai a ƙananan hukumomi, tare da bayar da ƙwai a kan farashi mai sauƙi —wanda zai iya rage farashin da ya kai N1,000 a kowane kiret.
A nasa jawabin shugaban PAN a Legas, Mojeed Iyiola, ya ce ana ci gaba da tattaunawa don ganin masu kiwo sun sami damar sayar da ƙwai a wuraren sayar da su ba tare da cajin wani ɓangare ba, wanda hakan zai sa shirin ya ɗore.
“Wannan shi ne don taimakawa talakawan Nijeriya da ke fama da kayan abinci na yau da kullum, idan muka cire ’yan kasuwan, farashin zai ragu, kuma yawancin iyalai za su iya sayen ƙwai,” inji Iyiola.
Duk da ɗan jin daɗi daga ƙoƙarin da gwamnatin tarayya ke yi na rage farashin masara—wani muhimmin sinadari a kiwon kaji—sauran muhimman abubuwan da suka haɗa da methylene, lysine, urea, da cake ɗin gyaɗa sun sami ƙaruwar farashin.
Iyiola ya bayyana cewa buhun methylene mai nauyin kilogiram 25, wanda a baya ana sayar da shi akan M25,000, yanzu ana sayar da shi kusan N150,000, wanda ke tasiri sosai kan farashin samar da abinci. Yayin da masara ke da kusan kashi 60 na abincin kiwon kaji, hauhawar farashin sauran sinadaran na ci gaba da shafar samar da kwai.
ƙungiyar na fatan sabon shirin ba wai kawai zai sauwaƙa wa masu amfani da kuɗi ba ne kaɗai ba, har ma da inganta kuɗaɗen shigar manoman cikin gida ta hanyar kawar da masu cin hanci da rashawa.
