Mun yi asarar shanu 340 a hannun ɓarayi a watan Yuli — Miyetti Allah

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah ta Nijeriya reshen Jihar Benuwe, a ranar Alhamis, ta bayyana cewa aƙalla shanu 340 na mambobinta ne aka sace a cikin watan Yuli na 2025.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren ƙungiyar na jiha, Ibrahim Galma ya fitar kuma aka rabawa manema labarai a Makurdi.

A cewar sanarwar, lamarin ya faru ne a garin Agatu da wasu sassan Ƙaramar hukumar Guma da ke Jihar Benuwe.

Galma ya kuma yi zargin cewa, ɓarayin shanu da ke afkawa jama’a a ƙaramar Hukumar Agatu sun faɗaɗa hare-harensu zuwa sassan Jihar Kogi.

“A ranar 19 ga Yuli, 2025 wasu da ake zargin ’yan ƙabilar unguwar Eguma ne a ƙaramar hukumar Agatu sun sace shanu 73 na wani Sale Abubakar (makiyayi Fulani), kuma har ya zuwa yanzu ba a ƙwato shanun ba.

“A ranar 21/7/2025 wani gungun masu aikata laifuka daga unguwar Agatu sun yi awon gaba da shanu 80 na Ardo Sarkin Fulanin Bagana, an yi awon gaba da shanun ne a Jihar Kogi, kusa da kan iyaka da ƙaramar hukumar Agatu ta Jihar Benuwe.

ɓarayin sun kwashe shanun zuwa ƙauyukan Agatu. Daga baya kuma, an ƙwato shanu 30 daga cikin 80 a Agatu, inda ba a iya gano 50 ba.

“A ranar 24 ga Yuli, 2025 wasu miyagu matasa ‘yan garin Agatu sun yi awon gaba da wasu shanu 213 na Garah Mobaba, hakan kuma ya faru ne a kan iyaka tsakanin Jihar Kogi da Ƙaramar hukumar Agatu ta Jihar Benuwe, haka kuma lamarin na faruwa a wasu sassan ƙaramar hukumar Guma ta Jihar Benuwe, inda aka samu rahotannin sace-sacen shanu da kuma kashe-kashen makiyaya.”

ƙungiyar ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta binciki lamarin, ta gurfanar da waɗanda suka aikata wannan aika-aika a gaban kotu, tare da biyan waɗanda lamarin ya shafa diyya domin samar da zaman lafiya da zaman tare.

Sanarwar ta ƙara da cewa, “Muna kira ga gwamnatin jihar Binuwe da ta binciki lamarin, ta kama waɗanda suka kai hare-haren, tare da biyan waɗanda lamarin ya shafa diyya domin samun zaman lafiya da zaman tare tsakanin manoma da makiyaya a yankunan.”

Da aka tuntuɓi shugaban ƙaramar hukumar Agatu, James Melɓin, ya tabbatar da cewa an kai rahoton lamarin, ya kuma yi kira ga jami’an tsaro da su ɗauki mataki. “Muna kira ga jami’an tsaro da su binciki lamarin,” inji Melɓin.

Sai dai mai baiwa gwamna shawara na musamman kan harkokin tsaro Joseph Har ya ce bai da masaniya kan wani harin satar shanu da aka yi a Agatu, amma ya yi magana kan halin da ake ciki a Guma.

“Abin da ya faru a wurin shi ne shanunsu sun shiga gonakin mutane sun lalata musu amfanin gona, sai muka je can muka kwashe shanun, amma da masu su zo suka biya kuɗin amfanin gonakin da aka lalata, muka sako musu shanun,” inji shi.

Shanun mallakin Sale Abubakar (makiyayin Fulani), kuma har ya zuwa yanzu, ba a ƙwato shanun da aka sace ba.

By ukarofi