Yadda wasu jihohi suka kashe biliyan N102 wajen sayen kayan alatu a Kasafin 2025

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Wasu jihohin Tarayyar Nijeriya guda 12 sun kashe jimillar zunzurutun kuɗi Naira Biliyan 102 a cikin kasafinsu na shekarar 2025, domin saka kayan alatu a gidajen gwamnati da sayen motocin alfarma, kamar yadda wani bincike da jaridar News Point Nigeria ta gudanar ya nuna.

Kashe-kashe kuɗaɗen, wanda ya bayyana a rahoton ayyukan kasafin kuɗi na farkon shekara na jihohi, ya shafi kashe kuɗaɗe masu yawa a kan sayen motocin alfarma samfuran Toyota Prado, samfuran Jeep, motocin Hiluɗ, da manyan sedans kamar Toyota Camry da Corolla.

Haka nan an haɗa su da adadi mai yawa don ginin masauki, gyare-gyaren gidan baƙi, da wuraren zama na jami’an gwamnati.

Jihar Legas wadda ke kan gaba a kasafin kuɗin ita ce ta kashe kimanin Naira Biliyan 33, inda Naira Biliyan 20.67 ya tafi wajen sayen ababen hawa ga ‘yan majalisa kaɗai.

Jihar ta kuma ware sama da Naira Biliyan 1.15 domin gyara matsugunin gwamnati a Alausa da Abuja, da kuma wasu Naira Biliyan 11 domin gyara ginin majalisar.

Jihar Delta ta biyo bayanta, inda ta Naira Biliyan 14.91, wanda ya haɗa da kashe Naira Biliyan 11.23 wajen motoci sama da 260, da suka haɗa da motocin alfarma da motocin ɗaukar kaya na ayarin gwamnan da kuma tsofaffin masu riƙe da muƙamai.

Wani Naira biliyan 2.73 kuma an ware shi donin gyaran gidajen kwana a faɗin Asaba, Warri, Legas, da Abuja.

Jihar Taraba ta kashe Naira biliyan 9.57 don inganta gidajenta. Daga cikin muhimman abubuwan da aka ware sun haɗa da Naira biliyan 3 don gina gidaje da dama a garuruwa shida, da kuma Naira biliyan 1.17 domin ginawa da kuma samar da kayan ɗaki na gidan mataimakin gwamnan.

Jihar Borno ta ware Naira biliyan 7.75, wanda ya haɗa da Naira biliyan 6.92 domin sayen motoci 50 da sauran buƙatun sufuri.

Gyaran gidajen kwana a jihar ya laƙume Naira miliyan 830.5, wanda ya haɗa da gidajen ma’aikata da gidajen baƙi.

Jihar Ondo ta kasafta Naira biliyan 7.51, inda Naira biliyan 3.95 ya tafi wajen sayen Toyota Fortuners guda 27, Corolla guda 13, Hiluɗ 5, da kuma wata motar sulke. Gyaran gidaje da ofisoshi sun laƙume Naira biliyan 1.33.

Jihar Adamawa ta ware Naira biliyan 6.46, inda aka ware Naira biliyan 2.9 domin sayen mota ƙirar SUV da Naira biliyan 3.56 domin inganta gidajen gwamna da mataimakin gwamna a Yola da Abuja.

Jihar Kebbi: Naira Biliyan 5.66 (motocin da za a saya wa majalisa da kuma inganta gidajenta a garuruwa huɗu).

Jihar Ekiti: Naira biliyan 5.16 (Gidajen gwamnati a Ado Ekiti da Abuja, da motoci 80 da suka haɗa da Prado Jeeps da JAC).

Jihar Kuros Riba: Naira biliyan 4.52 (gyara gidaje, 28 Toyota Prado na ‘yan majalisa).

Jihar Jigawa: Naira biliyan 3.39 (motoci na hukuma da gyare-gyare a faɗin gidan gwamna, ofisoshin jami’an gwamnati).

Jihar Yobe: Naira biliyan 2.91 (Manyan motocin Hiluɗ 30, gyaran gidan sarki da masauƙin manyan baƙi).

Jihar Imo: Naira biliyan 1.45 (gyara gidajen hukuma, motoci 58 da suka haɗa da Prado Jeeps na alƙalai da na ɗaukar ma’aikatan shari’a).

A halin da ake ciki kuma, ba a samu cikakken bayanin kashe maƙudan kuɗaɗe daga sauran jihohi 24 da kuma babban birnin tarayya ba, domin waɗancan jihohin sun kasa fitar da cikakkun rahoton aikin kasafin kuɗin.

Wannan lamari ya haifar da cece-kuce a kan abubuwan da suka shafi kasafin kuɗi, musamman yadda miliyoyin ‘yan Nijeriya ke fama da hauhawar farashin kayayyaki, rashin aikin yi, da gazawar ayyukan gwamnati.

By ukarofi