Gwamnonin 1999 sun buƙaci Tinubu ya samar da ayyuka ga matasa

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnonin jihohin Nijeriya da suka yi mulki daga shekarar 1999 zuwa 2007, sun buƙaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya mayar da hankali wajen kafa masana’antu.

Sun ce kafa kamfanoni a ƙananan hukumomi ne zai taimaka wajen samar da ayyukan yi fiye da rabon tallafin N5,000.

Tsofaffin gwamnonin sun bayyana hakan ne bayan ganawa da suka yi da shugaban ƙasa a Abuja, ƙarƙashin jagorancin tsohon gwamnan jihar Edo, Lucky Igbinedion, a ranar Juma’a.

Cif Igbinedion ya bayyana cewa sun tattauna batutuwan da suka shafi tsaro, tattalin arziki da kuma noma tare da miƙa shawarwarinsu ga shugaban ƙasa domin inganta rayuwar talakawa.

Tsofaffin gwamnonin sun bayyana cewa babu wata ci gaba da za a iya samu a ƙasar nan muddin tsaro bai inganta ba.

Sun jaddada cewa dole ne Gwamnatin Tarayya ta dauki matakai masu ƙarfi don daƙile matsalolin tsaro da suka addabi sassan ƙasar nan.

A cewar Igbinedion, “mun shaida wa Shugaban kasa cewa babu ci gaba ko zaman lafiya da za a samu matukar babu tsaro. Hakan ne ya sa muka buƙace shi da ya mayar da hankali wajen tabbatar da tsaro, domin hakan ne tushen komai a ƙasa.”

Tsofaffin gwamnonin sun ce raba N5,000 ga ‘yan ƙasa ba shi ne mafita ba, ganin cewa kuɗin ba zai iya ciyar da mutum ba ko sau daya a rana.

Sun buƙaci Tinubu da ya daina wannan salon tallafi maras ɗorewa, ya koma kan samar da abubuwa more rayuwa da za su kawo canji na hakika.

“Idan mutum ya samu N5,000 da safe, me zai ci da rana? Me zai ci da dare? Wannan ba mafita ba ce. Akwai buƙatar mu fuskanci gaskiya cewa waɗannan kuɗi ba sa magance matsalar talauci.”

ɗaya daga cikin manyan shawarwarin da tsoffin gwamnonin suka bayar shi ne gina masana’antun dogaro da kai a matakin ƙananan hukumomi 774 da ke faɗin ƙasar.

Sun jaddada cewa idan gwamnati ta ƙirƙiro masana’antun da za su ɗauki jama’a aiki, hakan zai fi amfani a rayuwar talaka fiye da rabon kuɗi.

By ukarofi