Mutuwar bazata da matakan kare kai

Spread the love

Fassara: AISHA ASAS

Masanin cututtukan zuciya kuma Bishop na Cocin Anglican a Jihar Enugu, Farfesa Rt. Rev. Samuel Ike, ya bayyana cewa, babban dalilin da ke haddasa mutuwar gaggawa a Najeriya shi ne halin rayuwa mara tsafta, rashin samun kulawar lafiya cikin sauki, da kuma jahiltar alamomin barazana ga lafiya.

Farfesan ya bayyana haka ne yayin wata lacca da aka gudanar a makarantar koyar da likitanci ta Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Enugu (ESUT), tare da haɗin gwiwar Gwamnatin Jihar Enugu, mai taken: “Annobar Mutuwar Gaggawa a Cikin Al’umma: Me Za Mu Iya Yi?”

A cewar Hukumar Labarai ta Najeriya (NAN), laccar na da nufin faɗakar da jama’a kan yawaitar irin wannan mutuwa, da kuma gabatar da hanyoyin rigakafi da magance matsalar.

Abincin waje na haifar da cutar gida:

A jawabin nasa, Farfesa Ike ya caccaki yadda mutane ke mayar da abinci na ƙasashen waje kamar su ‘fast food’ da ‘snacks’ a matsayin abincin yau da kullum, yana mai cewa hakan na janyo cututtuka masu nasaba da zuciya da jijiyoyin jiki.

Ya shawarci mutane da su fi karkata zuwa cin ‘ya’yan itatuwa da ganyayyaki maimakon cin abinci mai nauyi da sinadarai marasa amfani.

Alamomin farko da ya kamata a lura da su:

Farfesan ya bayyana cewa, mutuwar zuciya ta bazata na faruwa ne cikin sa’a guda da bayyanar wata matsala, wadda ke biyo bayan rashin numfashi, bugun zuciya da ba daidai ba, da kuma ciwon kirji, kuma ana iya ceton rai idan aka ɗauki mataki cikin gaggawa.

Ya kara da cewa: “Idan mutum ya riƙa jin ciwo a gefen hagu na kirji da kuma hannun hagu, to akwai yiwuwar barazanar mutuwa. Ya dace mutane su riƙa duba bugun zuciyarsu da kuma nauyin jikinsu akai-akai.”

Halaye masu hatsari: Daga shan taba zuwa rashin barci:

Ya bayyana wasu daga cikin halayen da ke janyo mutuwar gaggawa da suka hada da:

Shan taba sigari, amfani da miyagun kwayoyi, shaye-shaye, rashin motsa jiki ko yin motsa jiki fiye da ƙima kamar dagawa da ƙarfi da ‘press-up’.

Haka zalika, ya bayyana cututtuka kamar su:

Suga (diabetes), tumbi (obesity), ciwon zuciya, ciwon kwakwalwa (epilepsy), hawan jini da bugun zuciya (stroke). Da wasu cututtuka na jijiyoyi a matsayin manyan barazana ga lafiyar zuciya.

Matsaloli masu janyo mutuwa: Daga ciwon asma zuwa fushin dare:

Malam Ike ya ƙara da cewa, wasu dalilai kamar sanyi mai tsanani, farin ciki fiye da ƙima, damuwa, ciwon asma, gajiyar numfashi, rikicewar juna biyu, raunin kai da kuskuren zubar da ciki na iya haifar da mutuwa kwatsam.

A cewarsa, mafi yawan waɗanda mutuwa ke ɗauka kwatsam maza ne saboda halinsu na ƙin zuwa asibiti da ɓoye damuwa.

A cewar binciken da aka gudanar a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Najeriya (UNTH) tsakanin 2007 zuwa 2018, kaso 13.6 cikin 100 na mutuwa a lokacin sun kasance na gaggawa, inda 8 daga cikin mutum 29 kacal suka isa asibiti kafin su mutu.

Buƙatar gaggawa: Gwaje-gwaje, wayar da kai da sauran matakai:

Farfesa Ike ya buƙaci a samu tsarin kula da irin waɗannan matsaloli ta hanyar:

Tallafin gwamnati.

Kayan aikin asibiti na zamani.

Tashoshin yaɗa labarai da shirye-shiryen wayar da kai.

Samun lambobin gaggawa a wuraren jama’a.

Gwajin gado da tarin jini don fahimtar asalin mutuwa:

Farfesa Robsam Ohayi, masani a fannin Pathology da Forensics, ya buƙaci jama’a da su riƙa gudanar da gwajin autopsy da toɗicology domin gano musabbabin mutuwa da kuma tantance ko cutar gado ce ko a’a. Ya buƙaci Gwamnatin Enugu ta kafa ɗakin gwajin sinadarai (toɗicology lab), ganin babu ko guda a jihar.

Gwamnatin Jihar Enugu na ɗaukar mataki:

A nasa ɓangaren, Gwamna Peter Mbah ta bakin Kwamishinan Lafiya, Dakta George Ugwu, ya bayyana cewa, gwamnatin Enugu na gina cibiyoyin kiwon lafiya guda 260 a dukan mazaɓun siyasa na jihar, domin hana yaɗuwar irin waɗannan mutuwa.

Mashawarci na Musamman kan Lafiya, Dakta Yomi Jaiye, ya ce, an amince a ƙaddamar da koyar da CPR (Cardio Pulmonary Resuscitation) a dukan cibiyoyin lafiya domin ceto rayuka kafin su mutu gaba ɗaya.

“Mutum na iya faɗuwa amma ba ya nufin ya mutu ba, jinin da ke kai masa numfashi zuwa ƙwaƙwalwa ne ya tsaya. Da zarar an yi CPR da wuri, zai iya farfaɗowa,” inji shi.

Talauci ma na janyo kisan rai:

Shugaban Jami’ar ESUT, Farfesa Aloysius Okolie, ya ja hankalin jama’a da cewa, ba ciwon zuciya kaɗai ke kisa ba, har ma da talauci, damuwa, da rashin kulawa daga gwamnati.

By ukarofi