
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba Bola Tinubu ya karrama tawagar ƴan wasan kwando ta mata (D’Tigress) da kyautar ƙasa ta OON, da kuma Dala 100,000 da gida kowace ƴar wasa.
Shugaba Tinubu ya bayyana haka ne a lokacin ya karɓi baƙoncin tawagar a yammacin ranar Litinin a Fadar Shugaban Ƙasa biyo bayan du suka lashe kofin gasar AfroBasketWomen karo na biyar a jere.
D’Tigress ta yi nasar ne a lokacin da ta doke takwararta ta Mali a wasan ƙarshe da ci 78 da 64, lamarin da ya kai ta ga lashe gasar karo na bakwai a tarihinta.
A makon da ya gabata ne shugaban ƙasar ya sanar da karrama tawagarsa Super Falcons bayan lashe kofin WAFCON karo na 10 a tarihin ƙungiyar ƙwallon ƙafar.
