Shariar dillancin ƙwaya: Kwamitin bincike ya miƙa wa Gwamnatin Kano rahotonsa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Kwamitin da Gwamnatin Kano ta kafa don binciken zargin Kwamishinan Sufurin jihar, Ibrahim Namadi da hannu a belin Sulaiman Ɗanwawu, wanda ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi a jihar, ya miƙa wa gwamnati rahotonsa.

A yau Litinin kwamitin, ƙarƙashin jagorancin Barista Aminu Hussaini ya miƙa rahoton ga Sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Umar Farouk.

Saidai, babu dai cikakken bayanin abinda rahoton ya ƙunsa, amma matakin da gwamnati za ta ɗauka ne zai fayyace abinda kwamitin ya gano a binciken nasa.

A makon da ya gabata ne Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar ya kafa kwamitin, bayan da aka zargi Namadi da ƙarbar belin Ɗanwawu, a lokacin da ya yi yunƙurin tsaya masa a kotu.

Lamarin da ya haifar da cecekuce acikin al’umma musamman ƴan jihar, duba da yadda wasu ke ganin bai dace mutum mai matsayin kwamishina ya karɓi belin wanda ake zargi da taimaka wa ta’ammali da miyagun ƙwayoyi ba.

Akan haka wasu ke ta kiraye-kirayen tsige shi daga muƙaminsa.

By Babaji