Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal ta aike da wata tawaga mai ƙarfi wacce ta kai ziyarar ta’aziyya ga sabon Sarkin Katsinan Gusau, Alhaji Abdulkadir Ibrahim Bello bisa rasuwar mahaifinsa Marigayi Alhaji Ibrahim Bello tare da taya shi murnar naɗin da aka yi masa a matsayin Sarkin Katsinan Gusau na 16.
Rabi’atu Yusuf babbar sakatariyar yaɗa labarai a ofishin Uwargidan Gwamnan ta bayyana haka a cikin wata sanarwa da ta raba wa manema labarai a Gusau yau Litinin.
Tace, tawagar ta samu jagorancin Hajiya Larai Musa Lawal, inda ta miƙa saƙon ta’aziyyar Uwargidan Gwamnan ga Sarkin da iyalansa bisa rasuwar mahaifinsa.
Uwargidan Gwamnan ta bayyana Marigayi Sarkin Katsinan Gusau Alhaji Ibrahim Bello a matsayin wanda ya samu karɓuwa sosai a bisa kyakkyawan jagoranci da hidima ga masarautar Gusau da Jihar Zamfara baki ɗaya.
Da take jawabi a yayin ziyarar, Hajiya Larai ta nuna matukar juyayi tare da yin addu’ar Allah ya jiƙan marigayin.
Ta kuma miƙa saƙon taya murna ga mai martaba sabon sarkin Katsinan Gusau Alhaji Abdulkadir bisa naɗin da aka yi masa a matsayin Sarkin Gusau na 16, tare da yi masa fatan alheri da samun nasara a wannan sabon muƙamin nasa.
A nasa jawabin, sabon sarkin ya nuna jin daɗin sa da ziyarar da kuma yadda uwargidan Gwamnan ta mara masa baya, inda ya bayyana ta a matsayin ‘yar uwa tare da godewa Gwamna Dauda Lawal da ya ba shi sarautar.
Ya yi alƙawarin yiwa masarautar hidima da sadaukarwa da tawali’u a lokacin mulkin sa.
A wani labarin kuma, sanarwar ta bayyana cewa tawagar ta kai irin wannan ziyarar ta’aziyya ga Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Zamfara, Mai Martaba Sarkin Anka, Alhaji Attahiru Muhammad Ahmad, domin ta’aziyyar rashin marigayi Sarkin Katsinan Gusau.
Sarki Attahiru shima a nasa jawabin, ya yabawa uwargidan Gwamnan bisa kulawar da ta nuna, inda ya ce hakan na ƙara ƙarfafa haɗin kai da goyon baya a tsakanin masarautun gargajiya a jihar.
Tawagar ta ƙunshi mamba na dindindin, manyan mataimaka na musamman, masu ba da shawara na musamman, shugaban matan PDP na jiha, daraktoci, matan shugabannin ƙananan hukumomi da ‘yan majalisar jiha, mata ‘yan siyasa, da sauran fitattun mutane.
