Yanzu-yanzu: Rashidi Ladoja ya zama Sarkin Masarautar Ibadan na 44

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Majalisar masu naɗa sarki a Ibadan, ta nada Otun na Masarautar Ibadan, wato Rashidi Ladoja a matsayin sabon sarki wanda ya kuma shi ne na 44 a tarihinta.

An zaɓe shi ne a farfajiyar Masarautar da ke Oke-Aremo a Ƙaramar Hukumar Ibadan ta Arewa a Jihar Oyo.

Ladoja yana ɗaya daga cikin mahalarta taron bada sanarwar.

A yayin zaɓen sabon sarkin, Balogun na Masarautar, Oba Tajudeem Ajibola ya ce za su miƙa sunan Ladoja ga Gwamna Seyi Makinde na jihar domin tabbatarwa.

Haka kuma da dama daga mazauna Ibdan sun nuna amincewa da matakin tare bayyana farin cikinsu da fatan samun ci-gaba, kamar yadda IntelRegion ta ruwaito.

By Babaji