Mata 1,000 a Gombe sun samu horon kasuwancin intanet

Spread the love

Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe

Kamfanin Shalele Enterprise da ke Jihar Gombe ya ƙaddamar da wani gagarumin shirin horar da mata 1,000 a jihar kan yadda za su gudanar da kasuwancin su ta hanyar amfani da kafar sadarwar intanet daga gidajen su.

Da take jawabi a wajen ƙaddamar da shirin a jami’ar mallakar Jihar Gombe shugabar kamfanin, Hajjiya Maryam Ibrahim Jalo, ta bayyana cewa wannan shiri na nufin inganta rayuwar mata tare da ba su damar zama ’yan kasuwa masu dogaro da kansu ba tare da barin gidajen su ba.

Maryam tace za su koyawa matan ne yadda za su yi amfani da kafafen sada zumunta wajen tallata kayayyakin su na kasuwanci cikin sauƙi daga gida.

A cewar ta hakan zai taimaka musu wajen rage matsin lamba a cikin aure tare da kawo zaman lafiya tsakanin ma’aurata,” in ji ta.

Hajiya Maryam ta ƙara da cewa wannan shiri na ɗaya daga cikin matakan da kamfanin yake ɗauka domin bunƙasa tattalin arzikin mata a Jihar Gombe.

A nasa jawabi mai bai wa gwamnan Jihar Gombe Shawara na musamman kan ƙanana da matsakaitan sana’oi SMEs Alhaji Abdulwahab Sabo wanda ya wakilci Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta tallafa da kuma haɗe irin waɗannan shirye-shirye cikin tsare-tsarenta na bunƙasa matasa da mata.“

Yace gwamnati na alfahari da irin wannan aiki, kuma za ta tabbatar da cewa shirin ya samu cikakken goyon baya da tallafi don amfanar da al’ummar jihar, in ji shi.

A nasa jawabin, Daraktan yaɗa labarai na cibiyar kasuwanci ta Jihar Gombe, Malam Yusuf Haruna, ya yaba da shirin, yana mai cewa mata na taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban tattalin arzikin ƙasa.

Ɗaya daga cikin mahalarta shirin, Juwairiyya Mohammad, ta bayyana jin daɗin ta da wannan damar, tana mai cewa horon zai sauƙaƙa musu gudanar da harkokin kasuwancin su.“

Tace yana da kyau musamman ga mata masu kula da gida su dinga samun irin wannan horo domin basu damar haɗa nauyin gida da kuma gudanar da kasuwanci ba tare da fita ba,

Shirin ya samu halartar manyan ’yan kasuwa da ƙwararru a harkar kasuwanci ta intanet daga sassa daban-daban na jihar, waɗanda suka gabatar da darussa tare da nuna ƙwarewarsu ga mahalarta.

By ukarofi