Shirin Boska Pain-Free Day ya kai wa fiye da mutane 5,000 Tallafin Lafiya Kyauta a Yola

Spread the love

Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe

A wani muhimmin mataki na inganta harkar lafiya, kamfanin Dexa Medica, masu ƙera maganin saukar zafi na Boska, sun bayar da kulawar lafiya kyauta ga fiye da mutane 5,000 a Yola, Abuja, Kano, Onitsha, Ibadan, Legas da sauran wurare.

A lokacin shirin Pain-Free Day, an gudanar da ayyukan lafiya kyauta da suka haɗa da duba lafiyar ido, gwajin hawan jini, gwajin sukarin jini, tausa na jiki, raba tabarau kyauta da kuma bayar da magunguna masu muhimmanci.

Ana gudanar da wannan shiri duk wata a jihohi daban-daban domin inganta lafiyar al’umma tare da nuna godiya ga masu amfani da kayayyakin kamfanin.

Yayin taron, Thomas Leramo, jami’in TMP na Boska Group, ya jaddada cewa wannan shiri ya fi mayar da hankali ne ga ‘yan kasuwa da dama daga cikinsu ba sa samun lokaci na duba lafiyarsu saboda yawan aiki.

Haka kuma, Michael Ezeamaka wanda ya wakilci kamfanin ya bayyana cewa, “’Yan kasuwa muhimman ɓangare ne na al’umma kuma suna tallafawa al’amura na kasuwanci.

Wannan shiri wata hanya ce ta mayar da martani da kuma kula da lafiyar jama’a gaba ɗaya, ba wai ido kawai ba. Manufarmu ita ce mu kai mutane 10,000 a kowace al’umma da muka zaɓa.”

Likitan ido Dr. Okereke Victor Kinggem ya yi gargadin muhimmancin yin binciken ido akai-akai domin gano matsalolin ido kamar su glaucoma, cataract, da kuma presbyopia waɗanda galibi ba a gano su da wuri.

“Za mu raba tabarau fiye da guda 200 don taimaka wa waɗanda ke da matsalar karanta rubutu saboda tsufa.

Haka kuma muna yin gwajin glaucoma kuma muna tura masu matsala mai tsanani zuwa manyan asibitoci. Mutane da dama sun samu magani da jinya kyauta kan cututtukan ido,” in ji shi.

Jakadan Boska, Babangida Bako, ya bayyana yawan matsalar hawan jini tsakanin ‘yan kasuwa wadda galibi ba a gano ta.

“Ta hanyar wannan shiri, muna wayar da kai kan harkar lafiya tare da ƙarfafa mutane su riƙa ganin likita sannan muna bayar da magunguna kyauta,” in ji shi.

Daya daga cikin waɗanda suka amfana da shirin, Sadiq Maiganga, ya nuna godiya kan wannan aiki, yana kira ga sauran kamfanoni su bi irin wannan misali.

“Sun yi babban aiki. Allah ya saka da alheri. Sauran kamfanoni su ma su yi irin wannan domin tallafawa al’umma,” in ji shi.

Shirin Pain-Free Day na ci gaba da faɗaɗa ayyukansa, yana samar da muhimman hidimomin lafiya a sauran wurare daban-daban a Najeriya ciki har da Kaduna, Bauchi, Sokoto da Ilorin.

By ukarofi