Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Hon Kabir Ɗalhatu (shooter)na mazaɓar Galadima a ƙaramar hukumar kankiya ya ƙaddamar da waɗannan mataimakan na musamman tare da bada tallafi na kayan sana’a ga mata su 40 domin ƙarfafa sana’ar su.
Mataimakan na musamman da kansilan ya ɗauka za su taimaka masa a wajen bada shawarwari akan abinda ya shafi mazaɓar da sauran hidimomin siyasa.
Sannan mata guda 40 da aka ba tallafin sana’a an basu waken suya domin su inganta sana’ar su ta awara da suke gudanarwa yau da kullum domin su dogara da kansu.
Bugu da ƙari Hon. Kabir Ɗalhatu ya bada naira 500,000 ga iyayen jam’iyyar APC na mazaɓar Galadima B, dake cikin ƙaramar hukumar Kankia.
Daga ƙarshe kansilan ya sha alwashin ci gaba da irin wannan aikin alheri ga al’ummar mazaɓarsa, “ba zanyi k5asa a gwiwa ba, akan wannan aikin alheri,”kansilan ya faɗi haka.
Taron da aka gudanar a sakatariyal ƙaramar hukumar Kankia ya samu halartar shugaban kansiloli na ƙaramar hukumar Hon. Mansur Isa Rimaye, tsohon shugaban ƙaramar hukumar Hon. Musa Maikudi Kankia.
