Gwamna Raɗɗa ya taya sabbin hakimai da masarautar Katsina ta naɗa murna

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Wannan bayanin ya fito daga babban jami’in yaɗa labarai na gwamna, Muhammad kaula.

Gwamnan ya bayyana naɗin ya nuna yadda masarautar Katsina ta ke lura da cancanta,ƙwazo da mutumtaka kafin bada sarauta.

Gwamnan ya bayyana sabbin hakiman a matsayin ya’yan masarautar da suka sadaukar da rayuwar wajen aikin gwamnati da cigaban al’umma.

Gwamnan yayi fatan za suyi amfani da matsayin da Allah ya basu wajan kyautatawa al’ummar su da daga darajar gundumar su da jihar baki ɗaya.

Sabbin hakiman sun haɗa da Sanusi Kabir Usman ƙani ne ga Sarkin Katsina,a matsayin (Karshin Katsina) Hakimin Shinkafi da Ahamed Abdulmummuni Kabir Usman (Ɗan Majen Katsina)Hakimin Dankama.

Sai tsohon ministan sufuri Sanata Hadi Sirika (marusan)Hakimin Shargalle da Alhaji Abubakar Dardisu (Sarkin Mudurun Katsina) Hakimin Muduru.

Akwai Gambo Abdullahi Dabai (Dausayin Katsina) Hakimin Dabai da Muhammad Dikko Umar ɗa ga gwamna Dikko Raɗɗa (Gwagwaran Katsina) Hakimin Raɗɗa.

Nan gaba masarautar Katsina za ta sanar da ranar bikin naɗin hakiman.

By ukarofi