Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, a jiya Lahadi ya ƙaddamar da kamfen na dasa bishiyu miliyan biyar na 2025 a Dausayin Yanbawa da ke ƙaramar hukumar Makoɗa.
Wannan shiri na da nufin magance illolin sauyin yanayi, inganta muhalli, da kuma ƙarfafa ɗorewar lafiyar muhalli.
Yayin ƙaddamarwar, Gwamna Yusuf ya ce gwamnatinsa ta ƙuduri aniyar samar da bishiyu a faɗin Jihar Kano domin inganta sauyin yanayi.
Ya bayyana cewa farfaɗo da dausayin, wanda aka yi watsi da shi tun bayan da aka kafa shi a 1972, wani ɓangare ne na dabarun inganta sauyin yanayi da bunƙasa harkar noma na Jihar Kano.
A nashi ɓangaren, Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi na jihar, Dakta Dahir M. Hashim, ya baiyana cewa dashen bishiyun ya baiyana aniyar gwamnati ta farfaɗo da muhallin Jihar da kuma inganta sauyin yanayi.
“Tare da haɗin gwiwar masu ruwa da tsaki daga gwamnati da kuma masu zaman kansu, za mu haɗa ƙarfi da ƙarfe da dukkan ƙananan hukumomi 44 domin dasa itatuwa da kiyaye su a makarantu, wuraren ibada, gidaje, gonaki da filayen al’umma.
Ina kira ga dukkan al’umma, cibiyoyi, da masu ruwa da tsaki da su ɗauki wannan kamfen a matsayin nasu.
Tare, za mu iya tabbatar da makoma mai cike da koren ganyaye da lafiya ga Jihar Kano,” in ji Kwamishinan.
