Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
A ƙokarin ta na tsaftace babban birnin jihar, hukumar kare muhalli ta jihar (SEPA) ta gudanar da jerin ayyukan tsaftace muhalli kamar yadda ta saba.
Shugaban hukumar Kabir Usman Amoga wanda ya jagoranci ma’aikatan sa wajen tsaftace manyan wurare a cikin garin Katsina ya bayyana cewa manufar hukumar ita ce tabbatar da tsaftar muhalli musamman a wannan lokaci na damina, domin kaucewa yaɗuwar cututtuka da kuma toshe hanyoyin ruwa.
Ya tabbatar da cewa hukumar sa ba za ta gajiya ba wajen tsaftace manyan biranen jihar ta hanyar kwashe shara akai akai.
Amoga ya yi kira ga al’ummar jihar da su ba hukumar goyon baya ta hanyar zuba shara a wurare da hukumar ta tanada,su guji zuba shara a magujin ruwa.
Ya yaba wa Gwamna Dikko Raɗɗa bisa irin kulawa da yake baiwa hukumar.
Ayyukan hukumar ta gudanar sun haɗa da kwashe shara a gyaran wasu manyan wurare da ke cikin birnin Katsina.
Wuraren sun haɗa da Farin Masallaci,Daki tara,Gwan Gwan da bakin roundabout na Ladan Wafa.
Sauran sun haɗa da Sabon titin Saulawa,Lambusa, ƙofar yanɗaka da bakin roundabout na KSTA da kuma kwanar Ɗorawa.
Wannan mataki yana cikin ƙoƙarin da hukumar SEPA ke yi na wayar da kan al’umma game da muhimmancin tsafta da kare lafiyar jama’a
