Abuja: NCAA ta dakatar da direbobin jiragen sama kan saɓa wa dokar kulawa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Kula da Zirga-zirgar Jiragen Sama ta Ƙasa (NCAA) ta dakatar matuƙa jirage masu tashin angulu na ValueJet guda biyu bisa saɓa wa dokokin kulawa a filin Nnamdi Azikwe da ke Abuja.

A sanarwar da jami’inta na hulɗa da jama’a da kula da kwastomomi, Michael Achimugu ya fitar, hukumar ta ce lamarin ya auku ne sashen tashin jirage, ranar Juma’a, 5 ga Agusta.

Bincike ya nuna cewa matukan sun fara tashi ne daga wuraren ba tare da kammala cike ƙa’idodin tashi ba, lamarin da ta kira abinda ka iya jefa rayukan matukan da wasu cikin haɗari.

NCAA ta kuma ce, hakan saɓa wa dokar sufurin jiragen sama ta ƙasa da na kulawa a matakin ƙasa-da-ƙasa.

Don haka ta ƙwace lasisin Kyaftin Oluranti Ogoyi da Ivan Oloba har zuwa lokacin da za a kammala bincike akan lamarin.

By Babaji