Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
A jawabinsa a wajen taron, shugaban kwamitin, Honarabul Ibrahim Ɗanjuma Machika, ya bayyana cewa manufar taron ita ce ƙarfafa zumunci da haɗin kai tsakanin kwamitin da shugabannin ƙananan hukumomi, tare da tattauna batutuwan da suka shafi ci gaban al’ummar su da jihar musamman a matakin ƙananan hukumomi.
Ya ƙara da cewa, taron na da muhimmanci sosai domin bayar da dama ga ‘yan majalisar su fahimci matsaloli da ƙalubalen da shugabannin ƙananan hukumomi ke fuskanta a aikinsu na yau da kullum.
“Wannan zama zai taimaka wajen tsara hanyoyin magance matsaloli da kuma inganta gudanar da ayyukan ci gaba a matakin ƙasa,” inji Hon. Machika.
Kwamitin ya kuma tabbatar da cewa zai ci gaba da kasancewa tare da shugabannin ƙananan hukumomi domin tabbatar da ingantaccen shugabanci, gaskiya da riƙon amana a cikin harkokin mulki da walwalar al’umma.
Babu dai wani bayanin bayan taron.
