
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Aƙalla sama da gidan sauro guda 5,000 za a raba a mazaɓu 11 da ke Ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa a jihar Kano, a wani ɓangare na yaƙi da zazzaɓin cizon sauro da ake yi a faɗin jihar.
Jami’in da ke kula da harkokin samar da magunguna a ƙaramar hukumar, Alhaji Ibrahim Ayuba ya bayyana haka jim-kaɗan bayan ƙaddamar da shirin rabon gidan sauro a yankin.
A wata takarda daga jami’ar yaɗa labaran ƙaramar hukumar, Alhaji Ibrahim Ayuba, ya bayyana cewa an raba sassan karamar hukumar zuwa gudumomi daban-daban domin samun sauƙin gudanar da rabon gidan sauron.
Ya ce, daga cikin mazaɓun, mazaɓar Ɗanguguwa za ta samu gidan sauro kimanin 437, mazaɓar Dawaki ta Gabas na da gidan sauro 340, Dawaki ta Yamma ita ma tana da 329, sannan mazabar Dawanau za ta samu gidan sauro kimanin 520 inda mazabar Ganduje ke da gidan sauro 191, haka kuma Gagari na da gidan sauro 528, yayin da mazaɓar Jalli za ta samu guda 344, Kwa tana da 402, mazabar Marke 355, sannan mazaɓar Tattarawa tana da 317, sai kuma mazaɓar Tumfafi da take da guda 947.
Daga nan kuma Ibrahim Ayuba, ya yi karin haske dangane da masu korafin cewa ba a ba su katin da ake amfani da shi ba a wajen ba da gidan sauro.
“Ba gida- gida aka bi ba, kuma ba a gida za a ba su ba; ko’ina da na’ura ake amfani, sai dai su je gurin da aka gaya musu inda na’urar da za a yi musu amfani da ita take”, inji shi.
Sannan, ya kuma ba da tabbacin cewa za a bi kowane lungu da sako na karamar hukumar domin a kammala aikin cikin nasara wanda ya yi fatan al’ummar karamar hukumar za su ba da hadin-kansu.
Malama Furera Muhamdu Sani Kofar Yamma daga mazaɓar Dawaki ta Yamma, tana daya daga cikin wadanda suka amfana da gidan sauron.
“Kowa ya samu wannan gudan sauro ya adana, ya huta da zuwa asibiti a ce maleriya ce. In dai kana shiga gidan sauron nan wallahi ba kai ba zuwa asibiti Allah, Alhamdu Lillah.”






