Yadda zargin Atiku da mamaye ADC ya jefa ƴan ɓangaren Obi cikin damuwa

Spread the love

ADaga BELLO A. BABAJI a Abuja

Yayin da Nijeriya ke cigaba da kusantar babban zaɓen 2027, akwai yiwuwar samun ɓaraka acikin jam’iyyar adawa ta ADC da aka ƙarfafa ta haɗakar manyan siyasa.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar da ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, Peter Obi ke kan gaba wajen jan ragamar harkokin jam’iyyar.

Wasu muryoyi daga cikin jam’iyyar sun zargi Atiku da ƙoƙarin mamaye tsare-tsaren jam’iyyar cikin wani salo da nufin zama wanda zai tsaya takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar.

Lamarin da ya sa ƴan ɓangaren Obi suke ganin hakan a matsayin nuna ƙiyayya a gare su domin a cewarsu, an mayar da su saniyar ware wajen gudanar da muhimman al’amura a jam’iyyar.

Jam’iyyar da ake gani a matsayin wadda za ta zama babbar abokiyar karawa da mai mulki, wato APC a zaɓen shugaban ƙasa, ta fara samun tsaiko wanda ka iya haifar da rauni ga ɓangaren adawa.

Wani babban mamban ADC da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, Atiku ya mamaye sama da kaso 70 na tsare-tsaren jam’iyyar a matakin ƙasa da na jihohi.

Ya kuma ce, hakan ya samu ne sakamakon sake hannu ga jiga-jigan jam’iyyar domin tafiyar da alƙiblarta bisa tsari.

By Babaji