Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe
Al’ummar Talasse, hedikwatar ƙaramar hukumar Balanga a Jihar Gombe, na ci gaba da rayuwa cikin duhu shekaru 19 bayan katse musu wutar lantarki, inda suka bayyana ɓacin ran su bisa yadda aikin dawo da wutar lantarki da aka fara ya tsaya cak ba tare da wani bayani ba.
Aikin, wanda ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Billiri da Balanga, Hon. Ali Isa JC, ya ƙaddamar tun farkon wannan shekarar.
An fara da saita sanduna da shigar da na’urorin canja wuta (transformers), amma komai ya tsaya fiye da wata biyu da suka gabata. “Yan siyasa su kan zo da alƙawari, amma su ɓace bayan zaɓe,” in ji Yakubu Ayuba, mazaunin Talasse.
Ali JC ya faranta mana rai da wannan aiki, amma yanzu kamar ya biyo sahun sauran ‘yan siyasa ne.
Yakubu ya ce rashin bayanin halin da ake ciki daga ɗan majalisar ya ƙara rage musu ƙwarin gwiwa, yana mai cewa rashin wuta na rusa kasuwanci da cigaban yankin “Ba wuta, ba kasuwanci.
Wannan abin zai tasiri sosai a yadda zamu zaɓi shugabanni a 2027,” in ji shi.
Musa Adamu Galadima, wanda aka fi sani da Musa Tela, mai sana’ar ɗinki ya bayyana yadda rashin wutar lantarki ya durƙusar da kasuwancinsa. “Jenerata ya fi ƙarfin mu. Sai da na kori yaran da ke koyon sana’a a ƙarƙashina domin ba zan iya ci gaba da ɗaukar nauyin su ba.
Shi kuwa Sulaiman Idris, mai sayar da kayan Sanyi, ya ce: “Ina kashe naira dubu goma a rana wajen siyan ƙanƙara domin sanyaya lemo. Amma yanzu babu wuta, babu abokin ciniki.
Mun fara ganin cigaba lokacin da aka kawo kayan aiki, amma yanzu komai ya tsaya mun fara fidda rai.
Da aka tuntuɓe shi, Hon. Ali Isa JC ya tabbatar da tsaikon aikin. Ya danganta hakan da jinkirin sakin kuɗaɗen gwamnati ga kwangiloli.
“Mun tuntuɓi kamfanin da ke aikin. Matsalar ta samo asali ne daga jinkirin biyan kuɗaɗe daga gwamnatin tarayya. Muna ƙoƙarin ganin an hanzarta sako kuɗaɗen,” in ji shi.
A ɓangare guda kuma, gwamnatin Jihar Gombe ta fara aikin samar da wutar lantarki mai ƙarfin 620KW a dam ɗin Balanga, ta hanyar haɗa ƙaramin madatsar ruwa da hasken rana domin taimaka wa al’ummomin da suka jima suna fama da duhu.
Sai dai jama’ar Talasse sun bayyana matsayinsu na cewa ba wuta, babu ƙuri’a a zaɓen 2027.
